TAMBAYOYIN MATASA
Nuna Ladabi Yana da Muhimmanci Kuwa?
‘Mutane ba sa taimaka mini saboda haka, me zai sa in taimaka musu?’
‘Me zai sa ka dami kanka ka yi amfani da irin furucin nan “don allah,” da kuma “na gode”?’
‘Bai kamata na yi wa ’yan’uwana ladabi ba, da shi ke dukanmu iyali daya ne.’
Kana jin kai ma za ka iya fadan haka? Idan haka ne, to, ba ka san amfanin ladabi ba tukun!
Abin da ya kamata ka sani game da ladabi
Ladabi zai iya amfane ka a fannoni uku:
Halinka. Yadda ka ke bi da mutane zai sa mutane su san ko kana da hankali ko babu. Idan kana bi da mutane da ladabi za su san ka manyanta hakan zai sa su yi lababi gare ka! Amma idan kana rashin hankali wa mutane za su ce kai mai son kai ne, kuma hakan zai hana ka samun zarafi ko aikin albashi. Daidai ya ke da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai-jinƙai ya kan yi ma ransa alheri: Amma mai-bakin hali jiki nasa ya ke wahalarwa.”—Misalai 11:17.
Abokantaka. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku yafa kauna, gama ita ce magamin kamalta.” (Kolosiyawa 3:14) Hakan gaskiya ce game da abokantaka. Yana da sauki mutane su yi kusa da wadanda suke da ladabi kuma suke bi da su da kyau. Ko kai fa za ka so ka yi abokantaka da wani mai rashin kunya kuma marar hankali ne?
Yadda mutane suke bi da kai. Wata matashiya mai suna Jennifer, ta ce: “Idan kana ladabi kullum, a kwana a tashi har masu rashin hankali za su so su bi da kai cikin ladabi.” Amma idan kai ne ba ka hankali za ka sha wahalarsa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Da mudun nan da ku ke aunawa kuma da shi za a auna muku.”—Matta 7:2.
Batun shi ne: Babu rana da ba ma saduwa da mutane. Yadda ka ke bi da mutane haka nan za su bi da kai. A takaice, nuna ladabi yana da muhimmanci!
Yadda Za Ka Iya Yin Gyara
Ka yi ‘la’akari da ladabinka.’ Ka yi wa kanka wannan tambayar: ‘Ina daraja wadanda suka girme ni kuwa? Sau nawa nake iya ce “don allah,” ko kuma “na gode”? Ina maida hankali kuwa sa’ad da mutane ke magana da ni, ko ba na saurara har ma ina aika da sako a waya? Shin ba na daraja iyayena da ’yan’uwana saboda dukan “mu iyali daya” ne?’
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wajen ba da girma, kowa ya riga ba dan’uwansa.”—Romawa 12:10, Littafi Mai Tsarki.
Ka kafa makasudi. Ka rubuta abubuwan da za ka so ka yi gyara a kai. Alal misali, Allison ’yar shekara 15 ta ce: “Tana bukatar ta yi gyara a yadda take sauraron mutane.” David dan shekara 19, ya ce yana bukatar ya yi gyara a yadda yake aika da sako sa’ad da yake tare da iyalinsa ko abokansa. Ya ce: “Yin haka rashin hankali ne, yana nufin cewa ba na son jin maganarsu sai na wani dabam.” Edward dan shekara 17 ya ce: “Yana bukatar ya daina katse wa mutane maganar. Jennifer da aka ambata a baya ta ce za ta yi gyara a yadda take bi da tsofaffi. Ta ce: “Nakan ce ‘sannunku’ sai in nemi yadda ni da abokaina za mu wuce da sauri. Amma yanzu ina kokarin na yi abokantaka su. Yin haka ya sa na yi gyara a halina sosai!”
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowannenku kada ya kula da harkar kansa kawai, sai dai ya kula, har da ta dan’uwansa.”—Filibbiyawa 2:4.
Ka lura da yadda ka ke ci gaba. Ka bincika yadda za ka yi gyara a furucinka da halinka a cikin wata guda. Bayan haka ka lura ko ‘za a iya ganin gyarar a halayenka. Har ila, wace gyara nake bukatar yi?’ Ka jera makasudinka bi da bi.
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kamar yadda kuke so mutane su yi muku, ku yi masu hakanan kuma.”—Luka 6:31.