TAMBAYOYIN MATASA
Me Zan Yi Idan Aka Matsa Mini In Yi Lalata?
Wata ’yar shekara 21 mai suna Elaine ta ce: “A lokacin da nake makaranta, idan mutum ya ce ya yi jima’i, kowa sai ya ji kamar shi ma yana bukatar ya yi hakan. Balle ma babu wanda yake so a rika ganin cewa ya bambanta.”
Ka taba ji kamar kana bukatar ka yi jima’i domin kana ganin kowa yana yin hakan?
Masoyiyarka ko masoyinki ya taba matsa miki ku yi lalata?
Idan hakan, wannan talifin zai taimaka miki ki yanke shawara mai kyau idan wasu suna matsa miki ki yi lalata ko kuma idan kina sha’awar yin hakan.
Karya da kuma gaskiyar batun
KARYA: Kowa yana yin jima’i (ni kadai ne ba na hakan).
GASKIYAR BATUN: A wani bincike da aka yi a Amirka, matasa biyu a cikin matasa uku ’yan shekara 18 ne suka ce sun taba yin jima’i. Hakan yana nufin da yawa a cikinsu wato fiye da kashi 30 ba su taba yin hakan ba. Don haka, ba kowa ba ne yake yin jima’i.
KARYA: Yin jima’i zai karfafa dangantakarku.
GASKIYAR BATUN: Ko da yake wasu yara maza suna iya fadin hakan domin budurwa ta amince ta yi lalata da su, hakan ba gaskiya ba ne. A yawancin lokaci, saurayin da ya yi lalata da budurwa yakan rabu da ita. Hakan zai sa budurwar bakin ciki domin ta dauka cewa yana son ta kuma yana so su kasance tare. *
KARYA: Littafi Mai Tsarki ya ce jima’i bai dace ba.
GASKIYAR BATUN: Littafi Mai Tsarki ya amince mata da miji kadai su yi jima’i da juna.—Farawa 1:28; 1 Korintiyawa 7:3.
KARYA: Bin ka’idodin Littafi Mai Tsarki zai hana ni jin dadin rayuwa.
GASKIYAR BATUN: Yin jima’i kafin aure yana kawo da-na-sani ko bakin ciki ko kuma damuwa. Amma idan ka jira har sai ka yi aure kafin ka yi jima’i, za ka yi farin ciki.
Gaskiyar al’amarin: Yin jima’i kafin aure ya jawo wa mutane da yawa matsaloli. Amma yin aure kafin jima’i bai taba jawo wa kowa matsala ba.
Yadda za ka guji matsin yin lalata
Ka karfafa imaninka. Littafi Mai Tsarki ya ce mutanen da suka manyanta suna “iya bambanta nagarta da mugunta.” (Ibraniyawa 5:14) Irin mutanen nan suna da tabbaci, don haka, ba a iya saurin matsa musu su yi abin da bai dace.
Wata ’yar shekara 16 mai suna Alicia ta ce: “Ina yin iya kokarina don kada in bata sunana, kuma ina guje wa yanayin da zai iya sa hakan ya faru.”
Ka yi tunani a kan wannan: Da wane irin suna ne kake so mutane su san ka? Shin zai dace ka zub da mutuncinka don kana so mutane su so ka?
Ka yi tunanin sakamakon da hakan zai jawo. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba.” (Galatiyawa 6:7) Ka yi tunanin yadda rayuwarka da mutumin za ta kasance a nan gaba idan ka yi jima’i domin ana matsa maka. *
Wata ’yar shekara 16 mai suna Sienna ta ce: “Mutanen da suke yin jima’i kafin su yi aure, sukan yi da-na-sani daga baya, zuciyarsu takan dame su, kuma sukan ji kamar ba a kaunar su. Kari ga haka, suna iya yin cikin shege ko su kamu da cututtuka.”
Ka yi tunani a kan wannan: An yi wannan tambayar a wani littafi mai suna Sex Smart cewa: “Idan abokanka suna matsa maka ka yi abin da zai jawo maka bakin ciki, shin zai dace ka ci gaba da yin mu’amala da su kuma ka rika bin shawarwarin da za su ba ka a kan abubuwa masu muhimmanci a rayuwa?”
Ka kasance da ra’ayin da ya dace. Jima’i ba abu marar kyau ba ne. Littafi Mai Tsarki ma ya karfafa ma’aurata su ji dadin yin jima’i da juna.—Karin Magana 5:18, 19.
Wani dan shekara 17 mai suna Jeremy ya ce: “Jima’i abu mai kyau ne da Allah ya halitta. Allah yana so mu ji dadin yin hakan, bayan mun yi aure kawai.”
Ka yi tunani a kan wannan: Sa’ad da ka yi aure wata rana, za ka iya yin jima’i. Kuma za ka ji dadin hakan ba tare da sakamako marasa kyau da aka ambata dazu ba.
^ Hakika ba saurayi ne kadai zai iya matsa wa budurwa ta yi lalata da shi ba. A wasu lokuta, ’yan mata ma sukan matsa wa samari su yi lalata da su.
^ Wasu daga cikin sakamakon su ne, cikin shege ko kuma mutumin ya fuskanci shari’a idan ya yi lalata da wadda ba ta kai shekarun yin jima’i ba bisa doka.