TAMBAYOYIN MATASA
Shin Ya Dace In Yi Jarfa Ne?
Me ya sa mutane suke son yin jarfa?
Wani matashi mai suna Ryan ya ce, “a gani na, wasu jarfa da ake yi a jiki suna da kyau sosai.”
Dalilin da ya sa mutane suke yin zane a jikinsu zai shafi ra’ayinka game da yin hakan. Alal misali, wata matashiya mai suna Jillian ta ce: “Mahaifiyar wata yarinyar da nake zuwa makaranta tare da ita ta rasu sa’ad da take ’yar karama. Amma da yarinyar ta girma, sai ta zana sunan mahaifiyarta a bayan wuyarta. A gani na, irin wannan zanen yana da kyau.”
Ko da mene ne dalilinka, ya kamata ka yi tunani sosai kafin ka zana wani abu da zai zauna a jikinka har abada! Idan kana so ka zana wani abu a jikinka, wadanne tambayoyi ne za ka yi la’akari da su? Kuma wadanne ka’idodin Littafi Mai Tsarki ne za su taimaka maka ka yanke shawara mai kyau?
Wadanne tambayoyi ne ya kamata ka yi?
Mene ne illar yin zane a jiki? Wani dandalin Intane na Mayo Clinic ya ce, “jarfa, wato zane a jiki yana bata fatar mutum, kuma hakan zai iya sa ya kamu da wasu cuttuttuka da suke lalata fatar mutum. A wasu lokatai, kuraje suna iya fitowa a inda aka yi zanen kuma hakan zai sa mutum ya kamu da wata cutar da ake kira keloids (kumburin fata).” Kari ga haka, dandalin ya ce: “Idan akwai wata cuta a na’urar da aka yi maka zanen da ita, za ka iya kamuwa da cutar.”
Wane irin suna ne za ka yi wa kanka? Ko ka ki ko ka so, shigar da kake yi zai nuna irin halaye da kake da su. Zai nuna ko ka manyanta ko kai mai aminci ne ko kuma marar hankali. Wata matashiya mai suna Samantha ta ce: “Duk lokacin da na ga wanda ya yi zane a jikinsa, ina kallonsa a matsayin dan shaye-shaye da kuma dan fati.”
Melanie ’yar shekara 18 ta ce: “A gani na yin zane a jiki yana boye kyaun mutum. Ina ganin kamar wadanda suka yi zane a jikinsu ba sa son a san halinsu, shi ya sa suke boyewa ta wajen yin zane a jiki.”
Shin za ka ci gaba da son zanen da ka yi? Da shigewar lokaci, kiba ko kuma tsufa zai sa zanen ba zai yi kyau ba. Wani matashi mai suna Joseph ya ce: “Na ga wadanda suka yi zane a jikinsu sa’ad da suke matasa amma bayan shekaru da yawa, zanen bai da kyau sam.”
Wata matashi dan shekara 21 mai suna Allen ya ce: “Zane a jiki yakan zama tsohon yayi. Kana iya son zanen amma da shigewar lokaci, ba za ka so shi kuma ba.”
Abin da Allen ya fada gaskiya ne. Domin yayin da mutane suke girma, ra’ayinsu da abin da suke so da kuma yadda suke ji suna canjawa amma zanen da suka yi a jikinsu zai kasance muddar ransu. Wata matashiya mai suna Teresa ta ce: “Ba na son na yi zanen da zai rika tuna min da wawacin da na yi a dā kuma ba na son ya zama daya daga cikin abubuwan da zan yi da-na-sani a kai a nan gaba.”
Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da hakan?
Mutumin da ya manyanta yakan yi tunani sosai kafin ya yanke shawara. (Misalai 21:5; Ibraniyawa 5:14) Saboda haka, ka yi la’akari da wadannan ka’idodin Littafi Mai Tsarki game da yin zane a jiki.
Kolosiyawa 3:20: “Ku ’ya’ya, ku yi biyayya da iyayenku cikin kowane abu, gama wannan abin yarda ne cikin Ubangiji.”
Idan kana zama da iyayenka, mene ne sakamakon ki yin biyayya ga umurnansu?
1 Bitrus 3:3, 4: “Kada adonku ya zama ado na waje, wato su kitson gashi, da sa ado na zinariya, ko yafa tufafi masu ƙawa; amma ya zama ɓoyayyen mutum na zuciya, cikin tufafi waɗanda ba su lalacewa, na ruhu mai-ladabi mai-lafiya.”
A ganinka, me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ambata “ɓoyayyen mutum na zuciya”?
1 Timotawus 2:9: “Mata su yafa tufafi” da ya cancanta kuma su kasance masu hankali
Mene ne hakan yake nufi? Me ya sa zama mai hankali ya fi wani zane a jiki muhimmanci?
Romawa 12:1: “Ku miƙa jikinku hadaya rayayyiya, tsattsarka, abar karɓa ga Allah. Domin wannan ita ce ibadarku ta ainihi,” LMT.
Me ya sa yadda kake bi da jikinka yake da muhimmanci a wurin Allah?
Mutane da yawa sun yi la’akari da ka’idodin nan kuma hakan ya sa sun ki su yi zane a jikinsu. Sun sami abin da ya fi hakan muhimmanci. Teresa, wadda aka ambata dazu ta ce: “Idan akwai wata kalma ko furuci da kake so, sai ka rika yin amfani da su. Idan kuma akwai wani mutumin da kake so sosai, ka gaya wa mutumin cewa yana da muhimmanci a gare ka. Maimakon ka zana wani abu a jikinka, ka bi abin da ka yi imani da shi.”