Koma ka ga abin da ke ciki

TAMBAYOYIN MATASA

Yaya Shigata Take?

Yaya Shigata Take?

 Me ya sa ya kamata ki kula da irin shigar da kike yi? Domin tufafi da muke sakawa na bayyana wa mutane halinmu. Mene ne irin shigarki take bayyana wa mutane?

 Kurakurai uku da mutane suke yi game da kayan yāyi da kuma yadda za ki guje musu

Kuskure na #1: Koya irin shigar da ya kamata ki yi daga hanyoyin sadarwa.

 Theresa ta ce: “A wasu lokuta, nakan yi sha’awar wasu riguna domin na kalli yadda ake tallace-tallacen su. Idan zuciyarki ta cika da tunanin wani irin rigar da mutane suke sakawa, hakan zai iya sa ke ma ki sayi rigar.”

 Wani littafi mai suna The Everything Guide to Raising Adolescent Boys ya ce: “’Yan maza suna son kayan yāyi kamar yadda ’yammata suke so. ’Yan kasuwa suna kokarin su rinjayi ’yan maza tun suna kanana.”

 Matakin da ya dace: Littafi Mai Tsarki ya ce: “Marar wayo yana gaskata kowace magana: Amma mai hankali yakan lura da al’amuransa da kyau.” (Misalai 14:15) Bisa ga wannan ka’idar, ki yi hattara da tallace-tallace da kike kallo. Alal misali, idan kika ga tallace-tallace game da tufafi da suke ta da sha’awa, ki tambayi kanki:

  •  ‘Wane ne zai amfana idan na bi wannan yāyi?’

  •  ‘Yin hakan zai kwatanta ni da wane irin salon rayuwa ne?’

  •  ‘Salon rayuwar nan tana bayyana ainihin halina kuwa?’

 Taimako game da kayan yāyi: A mako guda, ki kalli tallace-tallacen kayan yāyi da ake yi. Wane irin salon rayuwa ne suke daukakawa? Tallace-tallacen suna sa ki ji kamar ya kamata ki bi wannan salon ne? Wata matashiya mai suna Karen ta ce: “Ana yaudarar matasa su mai da hankali sosai ga yin hadadden ado da saka hadadden tufafi da kuma kasance da ‘hadadden’ siffa. ’Yan kasuwa da suka fahimci hakan suna samun kasuwa sosai a wurin matasa.”

Kuskure na #2: Yin wani irin shiga don ki zama kamar kowa.

 Wani matashi mai suna Manuel ya ce: “Idan ana yayin wani irin tufafi, kowa zai so ya sa tufafin. Idan ba ka sa irin tufafin ba, mutane za su yi maka ba’a.” Wata matashiya mai suna Anna ta ce: “Mutane sun fi damuwa ne da yadda za su zama kamar sauran mutane, ba wai sun damu da saka kayan yāyi kawai ba.”

 Matakin da ya dace: Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada ku biye wa zamanin nan.” (Romawa 12:2, Littafi Mai Tsarki) Bisa ga wannan umurnin, ki duba akwatin tufafinki kuma ki tambayi kanki:

  •  ‘Mene ne ainihi yake shafan irin shigar da nake yi?’

  •  ‘Shin, ina sha’awar kayan yāyi?’

  •  ‘Ina son burge mutane da tufafina ne?’

 Taimako game da kayan yāyi: Maimakon ki dauka kamar riguna sun kasu kashi biyu ne kawai, wato wadanda ake yāyinsu da kuma wadanda suka zama tsohon yāyi, ki tuna cewa akwai kashi da za su iya sa ki kasance da gaba gadi. Idan kika amince da irin shigar da kike yi ba za ki damu da irin shigar da mutane suke yi ba.

Kuskure na #3: Yin tunani cewa ‘yin shiga mai ta da sha’awa ya fi dacewa.’

 Wata matashiya mai suna Jennifer ta ce: “A gaskiya, a wasu lokuta nakan yi sha’awar saka tufafin da ba su dace ba.”

 Matakin da ya dace: Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kada adonku ya zama na kwalliyar kitso . . . sai dai ya zama na hali.” (1 Bitrus 3:3, 4, Littafi Mai Tsarki) Bisa ga wannan umurnin, ki yi tunanin abin da ya fi kyau, kyan fuska kawai ko kuma ainihin hali mai kyau?

 Taimako don ado: A alamance, kayan kwalliya mafi kyau shi ne filako. A gaskiya mutane ba sa damuwa da wannan halin a yau. Amma ki yi tunanin wannan:

 Kin taba yin tadi da wata da ta cika magana kuma duk maganar da take yi game da kanta ne kawai? Abin bakin ciki shi ne, mai yiwuwa ba ta san cewa tana sa ki fushi ba.

Kamar yadda yake da yin tadi, riguna masu nuna tsiraici suna iya sa mutane ganin kamar ke mai mutuwar so ‘ki jawo hankalin mutane’ ne, kuma hakan na iya bata wa mutane rai

 Idan kika saka riguna marasa mutunci, za ki zama kamar yarinyar nan. Tufafinki na iya jawo hankalin mutane, kamar dai kina ce musu ‘ku kalle ni,’ kuma hakan na iya sa mutane ji kamar ba ki da gaba gadi ko kuma kin damu da kanki ne kawai. Kari ga haka, zai iya sa wasu su ga kamar kina mutuwar jan hankalin mutane, ko da mutane marasa kirki ne.

 Maimakon ki yi tallar abin da ba za ki sayar ba, zai fi miki alheri ki kasance da filako. Wata matashiya mai suna Monica ta ce: “Kasancewa mai filako ba ya nufin za ki rika yin irin adon tsofaffi. Amma yana nuna cewa za ki yi ado a hanyar da zai nuna kina girmama kanki da kuma makwabtanki.”