Annabce-annabce Game da Almasihu Sun Nuna Cewa Yesu Ne Almasihu Kuwa?
Amsar Littafi Mai Tsarki
E. Da Yesu yake duniya, ya cika annabce-annabce da yawa da aka yi game da “Shugaba Wanda Aka Kebe,” wanda zai zama “Mai Ceton duniya.” (Daniyel 9:25; 1 Yohanna 4:14) Bayan mutuwarsa ma ya ci gaba da cika wasu annabce-annabcen.—Zabura 110:1; Ayyukan Manzanni 2:34-36.
Mene ne ma’anar “Almasihu”?
Kalmar Ibranancin nan Ma·shiʹach (Almasihu) da kalmar Helenancin nan Khri·stos (Kristi) duk suna nufin, “Wanda Aka Nada.” Saboda haka, “Yesu Kristi” yana nufin “Yesu Wanda Aka Nada,” ko kuma “Yesu Almasihu.”
A zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, idan mutum yana so ya nada wani, yakan dauki mai ya zuba a kan wanda ake so a ba shi damar yin wata hidima ta musamman. (Littafin Firistoci 8:12; 1 Sama’ila 16:13) Allah ne ya nada Yesu ya zama Almasihu, kuma matsayi ne babba. (Ayyukan Manzanni 2:36) Amma ba mai ne Allah ya yi amfani da shi wajen nada Yesu ba, ya nada shi da ruhu mai tsarki.—Matiyu 3:16.
Mutum daya ne kadai ya cika annabce-annabcen da aka yi game da Almasihu?
E. Kamar yadda zanen da ke yatsar mutum ba daya ba ne da wani, haka ma mutum daya ne kadai zai iya cika annabce-annabcen da aka yi game da Almasihu ko Kristi. Amma Littafi Mai Tsarki ya yi mana gargadi cewa, “Almasihan karya da annabawan karya za su fiffito, su yi manyan alamu da ayyukan ban mamaki domin su rude mutane, har da wadanda aka zaba in zai yiwu.”—Matiyu 24:24.
A nan gaba ne Almasihu zai bayyana?
A’a. Littafi Mai Tsarki ya yi annabci cewa daga zuriyar Sarki Dauda ne Almasihu zai fito. (Zabura 89:3, 4) Amma a yau babu littattafan tarihi da za su nuna wadanda suka fito daga zuriyar Dauda. Da alama Romawa sun kona su a lokacin da suka halaka Urushalima a shekara ta 70 bayan haihuwar Yesu. a Tun daga lokacin, ba wanda zai iya nuna shaida cewa shi daga zuriyar Dauda ne. Akasin haka, da Yesu yake duniya akwai littattafan nan, kuma har makiyansa ba su iya sun nuna cewa bai fito daga zuriyar Dauda ba.—Matiyu 22:41-46.
Annabce-annabce nawa ne aka yi game da Almasihu a Littafi Mai Tsarki?
Ba za mu iya ce ga yawan annabce-annabcen da aka yi game da Almasihu ba. Yadda ake lissafta annabce-annabce game da Almasihu ya bambanta. Alal misali, littafin Ishaya 53:2-7 ya ambaci abubuwa da dama da za su sa a gano Almasihu. Wasu za su iya cewa annabci daya ne a ayoyin nan, wasu kuma su ce annabce-annabce dabam-dabam ne.
Wasu annabce-annabce game da Almasihu da suka cika a kan Yesu
Annabci |
An rubuta a |
Yadda ya cika |
---|---|---|
Daga zuriyar Ibrahim |
Farawa 22:17, 18 |
Matiyu 1:1 |
Daga zuriyar Ishaku, dan Ibrahim |
Farawa 17:19 |
Matiyu 1:2 |
Daga zuriyar Yahuda Baisra’ile |
Farawa 49:10 |
Matiyu 1:1, 3 |
Daga zuriyar Sarki Dauda |
Ishaya 9:7 |
Matiyu 1:1 |
Budurwa ce ta haife shi |
Ishaya 7:14 |
Matiyu 1:18, 22, 23 |
A Bai’talami aka haife shi |
Mika 5:2 |
Matiyu 2:1, 5, 6 |
An kira shi Immanuel b |
Ishaya 7:14 |
Matiyu 1:21-23 |
Iyayensa talakawa ne |
Ishaya 53:2 |
Luka 2:7 |
An kashe kananan yara bayan da aka haife shi |
Irmiya 31:15 |
Matiyu 2:16-18 |
An kira shi daga kasar Masar |
Hosiya 11:1 |
Matiyu 2:13-15 |
An kira shi Banazarat c |
Ishaya 11:1 |
Matiyu 2:23 |
An aiko wani don ya shirya zuwansa |
Malakai 3:1 |
Matiyu 11:7-10 |
An nada shi Almasihu a shekara ta 29 bayan haihuwar Yesu d |
Daniyel 9:25 |
Matiyu 3:13-17 |
Allah ya kira shi Dansa |
Zabura 2:7 |
Ayyukan Manzanni 13:33, 34 |
Ya nuna himma don gidan Allah |
Zabura 69:9 |
Yohanna 2:13-17 |
Mai shelar labari mai dadi |
Ishaya 61:1 |
Luka 4:16-21 |
Hidimarsa a Galili ya zama kamar haske |
Ishaya 9:1, 2 |
Matiyu 4:13-16 |
Ya yi ayyukan al’ajabi kamar Musa |
Maimaitawar Shari’a 18:15 |
Ayyukan Manzanni 2:22 |
Ya koyar da ra’ayin Allah kamar yadda Musa ya yi |
Maimaitawar Shari’a 18:18, 19 |
Yohanna 12:49 |
Ya warkar da marasa lafiya da yawa |
Ishaya 53:4 |
Matiyu 8:16, 17 |
Bai daukaka kansa ba |
Ishaya 42:2 |
Matiyu 12:17, 19 |
Ya tausaya wa wadanda aka wulakanta su |
Ishaya 42:3 |
Matiyu 12:9-20; Markus 6:34 |
Ya nuna cewa Allah mai adalci ne |
Ishaya 42:1, 4 |
Matiyu 12:17-20 |
Mai Ba da Shawara Mai Ban Mamaki |
Ishaya 9:6, 7 |
Yohanna 6:68 |
Ya sanar da sunan Jehobah ko Yahweh |
Zabura 22:22 |
Yohanna 17:6, Tsohuwar Hausa a Saukake |
Ya yi amfani da misalai sosai a koyarwarsa |
Zabura 78:2 |
Matiyu 13:34, 35 |
Ya zama Shugaba |
Daniyel 9:25 |
Matiyu 23:10 |
Mutane da yawa ba su yi imani da shi ba |
Ishaya 53:1 |
Yohanna 12:37, 38 |
Ya zama dutsen tuntube |
Ishaya 8:14, 15 |
Matiyu 21:42-44 |
Mutane sun ki shi |
Zabura 118:22, 23 |
Ayyukan Manzanni 4:10, 11 |
An tsane shi babu dalili |
Zabura 69:4 |
Yohanna 15:24, 25 |
Ya shiga Urushalima a matsayin sarki a kan jaki |
Zakariya 9:9 |
Matiyu 21:4-9 |
Yara sun yabe shi |
Zabura 8:2 |
Matiyu 21:15, 16 |
Ya zo cikin sunan Jehobah |
Zabura 118:26 |
Yohanna 12:12, 13 |
Amininsa ya ci amanarsa |
Zabura 41:9 |
Yohanna 13:18 |
An sayar da shi a kan azurfa 30 e |
Zakariya 11:12, 13 |
Matiyu 26:14-16; 27:3-10 |
Abokansa sun gudu sun bar shi |
Zakariya 13:7 |
Matiyu 26:31, 56 |
An ba da shaidar karya a kansa |
Zabura 35:11 |
Matiyu 26:59-61 |
Bai tanka wa masu zarginsa ba |
Ishaya 53:7 |
Matiyu 27:12-14 |
An tufa masa miyau |
Ishaya 50:6 |
Matiyu 26:67; 27:27, 30 |
An buge shi a kai |
Mika 5:1 |
Markus 15:19 |
An yi masa bulala |
Ishaya 50:6 |
Yohanna 19:1 |
Bai yi fada da wadanda suka mare shi ba |
Ishaya 50:6 |
Yohanna 18:22, 23 |
Masu mulki sun hada baki sun kulla masa sharri |
Zabura 2:2 |
Luka 23:10-12 |
An kafa hannuwansa da kafafunsa a kan gungume da kūsa |
Zabura 22:16 |
Matiyu 27:35; Yohanna 20:25 |
An jefa kuri’a (yi caca) a kan rigarsa |
Zabura 22:18 |
Yohanna 19:23, 24 |
An lissafta shi a cikin masu zunubi |
Ishaya 53:12 |
Matiyu 27:38 |
An zage shi kuma an yi masa bakar magana |
Zabura 22:7, 8 |
Matiyu 27:39-43 |
Ya sha wuya don masu zunubi |
Ishaya 53:5, 6 |
1 Bitrus 2:23-25 |
Kamar dai Allah ya yi watsi da shi |
Zabura 22:1 |
Markus 15:34 |
An ba shi ruwan tsami da wani abu mai daci ya sha |
Zabura 69:21 |
Matiyu 27:34 |
Ya ji kishin ruwa kafin ya mutu |
Zabura 22:15 |
Yohanna 19:28, 29 |
Ya bar ransa a hannun Allah |
Zabura 31:5 |
Luka 23:46 |
Ya mutu |
Ishaya 53:12 |
Markus 15:37 |
Ya ba da fansa don gafarar zunubai |
Ishaya 53:12 |
Matiyu 20:28 |
Ba a karya kasusuwansa ba |
Zabura 34:20, Tsohuwar Hausa a Saukake |
Yohanna 19:31-33, 36 |
An soke shi |
Zakariya 12:10 |
Yohanna 19:33-35, 37 |
An binne shi a wurin binne masu arziki |
Ishaya 53:9 |
Matiyu 27:57-60 |
Allah ya ta da shi daga mutuwa |
Zabura 16:10 |
Ayyukan Manzanni 2:29-31 |
Wani ya dauki matsayin wanda ya ci amanarsa |
Zabura 109:8 |
Ayyukan Manzanni 1:15-20 |
Ya zauna a hannun damar Allah |
Zabura 110:1 |
Ayyukan Manzanni 2:34-36 |
a Littafin nan, Cyclopedia of Biblical, Theological, and Ecclesiastical Literature, ya ce: “Ba abin shakka ba ne cewa a lokacin da aka halaka Urushalima ne aka halaka littattafan tarihi da ke dauke da sunayen iyalan Yahudawa. Ba kafin lokacin aka yi hakan ba.”
b A Ibrananci, sunan nan Immanuel yana nufin “Allah Yana Tare da Mu,” kuma hakan ya dace da matsayin Yesu na Almasihu. Zuwansa duniya da kuma ayyukan da ya yi sun nuna cewa Allah yana tare da bayinsa.—Luka 2:27-32; 7:12-16.
c An dauko kalmar nan, “Banazarat” daga kalmar Ibranancin nan neʹtser, kuma tana nufin “sabon reshe.”
d Don karin bayani a kan abubuwa da suka faru a lokuta dabam-dabam da suka nuna cewa Almasihu zai bayyana a shekara ta 29 bayan haihuwar Yesu, ka duba talifin nan, “Yadda Annabcin Daniel Ya Bayyana Zuwan Almasihu.”
e A littafin Zakariya ne aka rubuta annabcin nan, amma da Matiyu yake rubuta labarin, ya ce “abin da annabi Irmiya ya fada” ne. (Matiyu 27:9) Da alama cewa a wasu lokuta, littafin Irmiya ne ake sakawa farko a cikin Nassosin da ake kira “Littattafan Annabawa.” (Luka 24:44) Mai yiwuwa duka littattafan nan ne Matiyu yake kira littafin “Irmiya,” kuma littafin Zakariya yana cikinsu.