Koma ka ga abin da ke ciki

Mece ce Babila Babba?

Mece ce Babila Babba?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

 Littafin Ru’ya ta Yohanna ya nuna cewa Babila Babba ita ce dukan addinan karya da Allah ya tsana. a (Ru’ya ta Yohanna 14:8; 17:5; 18:21) Ko da yake wadannan addinan sun bambanta da juna, amma dukansu suna sa mutane su kauce daga bauta wa Allah na gaskiya, wato Jehobah.—Kubawar Shari’a 4:35.

Hanyoyin da za ka iya gane Babila Babba

  1.   Babila Babba alama ce. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta ta da “mace” da kuma “babbar karuwa” wanda ke da sunan “asiri, Babila Babba.” (Ru’ya ta Yohanna 17:1, 3, 5) An bayyana abubuwa a littafin Ru’ya ta Yohanna a alamance, hakazalika Babila Babba alama ce da ke bayyana wani abu, ba mace na zahiri ba ne. (Ru’ya ta Yohanna 1:1) Kari ga haka, tana “zaune bisa ruwaye masu-yawa” shi kuma na nufin, “al’ummai ne da taron jama’a, da dangogi da harsuna.” (Ru’ya ta Yohanna 17:1, 15) Mace na zahiri ba za ta iya yin hakan ba.

  2.   Babila Babba tana wakiltar wani abu ne da ke fadin duniya. Ita ce ake kira ‘babban birnin, wanda ke mulki bisa sarakunan duniya.’ (Ru’ya ta Yohanna 17:18) Saboda haka, an san da ita a duk duniya.

  3.   Babila Babba tana wakiltar addini ne ba siyasa ba ko kuma kasuwanci. Babila ta dā sananniyar birni ne da aka sani da yawan ‘sihiri’ da kuma amfani da ‘layu.’ (Ishaya 47:1, 12, 13; Irmiya 50:1, 2, 38, Littafi Mai Tsarki) Mutanen da ke birnin sun ci gaba da bin addinin karya, kuma hakan yana sabani da koyarwar Allah na gaskiya, Jehobah. (Farawa 10:8, 9; 11:2-4, 8) Masu mulki a zamanin suna ganin sun ma fi karfin Jehobah da kuma bautarsa. (Ishaya 14:4, 13, 14; Daniyel 5:2-4, 23) Hakazalika, an san Babila Babba da ‘sihiri.’ Hakan ya nuna cewa tana wakiltar wani rukunin addini ne.—Ru’ya ta Yohanna 18:23.

     Ba za a iya cewa Babila Babba wata kungiyar siyasa ba ce domin “sarakunan duniya” suna makokin halakarta. (Ru’ya ta Yohanna 17:1, 2; 18:9) Hakazalika, ita ba kungiyar ’yan kasuwa ba ne domin Littafi Mai Tsarki ya nuna bambancin ta da “dillalan duniya.”—Ru’ya ta Yohanna 18:11, 15.

  4. Hoton Sarkin Babila mai suna Nabonidus a jikin wani dutse tare da alamun da ke nuna alloli uku wato, Sin da Ishtar da kuma Shamash

      Babila Babba ta dace da addinin karya. Maimakon su koyar da mutane yadda za su kusaci Allah, Jehobah, addinin karya tamkar tana sa mutane bautawa allolin karya. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta wannan yanayin da “karuwanci.” (Levitikus 20:6; Fitowa 34:15, 16) A Babila ta dā koyarwar Allah-uku-cikin daya da kurwa marar mutuwa da kuma amfani da gumaka wajen bauta ya rufe ko’ina, kuma haka yake da addinan karya a yau. Wadannan addinan suna hada bautarsu da son kayan duniya. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta hakan da zina.—Yakub 4:4.

     Yadda addinan karya suke nuna son kayan duniya, ya yi daidai da yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Babila Babba cewa tana sanye da “tufafi masu ruwan jar garura” da kuma “ado da kayan zinariya, da duwatsun alfarma, da lu’ulu’u.” (Ru’ya ta Yohanna 17:4, LMT) Babila Babba ita ce tushen “abubuwa masu-ban ƙyama na duniya” ko kuma koyarwar karya da duk wani abu da ke bāta sunan Allah. (Ru’ya ta Yohanna 17:5) Mabiyan addinin karya su ne ‘al’ummai da taron jama’a, da dangogi da harsuna’ da suke goyon bayan Babila Babba.—Ru’ya ta Yohanna 17:15.

 Babila Babba ce ke da alhakin “dukan wadanda aka kashe a duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 18:24) A duk tarihin ’yan Adam an gano cewa ba kawai addinan karya ne ke haddasa yake-yake da ta’addanci ba, amma ba sa koyar da gaskiya game da Jehobah, Allah mai kauna. (1 Yohanna 4:8) Wannan ne dalilin da ya sa ake yawan kashe-kashe. Don wannan dalilin ne ya sa wadanda suke so su faranta wa Allah rai ya kamata su “fito daga cikinta,” suna ware kansu daga addinin karya.—Ru’ya ta Yohanna 18:4; 2 Korintiyawa 6:14-17.

a Ka duba talifin nan “Ta Yaya Zan Gane Addini na Gaskiya?