Allah Dunƙulin-Alloli-Uku ne?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Ɗarikoki da yawa na Kiristoci suna koyar cewa Allah Dunƙulin-Alloli-Uku ne. Amma, ka lura da abin da littafin Encyclopædia Britannica ya ce: “Furucin nan Dunƙulin-Alloli-Uku ko kuma koyarwar nan bai bayyana ba cikin Sabon Alkawari . . . A hankali ne koyarwar ta shiga bayan ƙarnuka da yawa kuma tare da jayayya da yawa.”
Hakika, ba a taɓa kwatanta Allah na Littafi Mai Tsarki cewa ɓarin Dunƙulin-Alloli-Uku ba ne. Ka lura da waɗannan ayoyi na Littafi Mai Tsarki:
“Ubangiji Allahnmu Ubangiji ɗaya ne.”—Kubawar Shari’a 6:4.
‘Kai, wanda sunanka Jehobah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.’—Zabura 83:18.
“Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya, da shi kuma wanda ka aiko, Yesu Kristi.”—Yohanna 17:3.
“Allah ɗaya ne.”—Galatiyawa 3:20.
Me ya sa yawancin ɗarikokin Kirista suke ce Allah Dunƙulin-Alloli-Uku ne?