Mene Ne Lambar Nan 666 Take Wakilta?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Littafin Ru’ya ta Yohanna ta ce lambar nan 666 sunan wata dabba ce mai kawuna bakwai da kahoni goma, wadda ta fito daga cikin teku. (Ru’ya ta Yohanna 13:1, 17, 18) Wannan dabbar tana wakiltar duk wata gwamnatin da ’yan Adam suka kafa don yin mulki bisa “kowace kabila da al’umma da kowane harshe.” (Ru’ya ta Yohanna 13:7) Lambar 666 tana nuna yadda gwamnatocin da ’yan Adam suka kafa sun kasa a gaban Allah. Ta yaya?
Ma’anar lambar. Dukan sunayen da Allah ya bayar suna da ma’ana. Alal misali, Allah ya ba Abram (ma’ana “An Daukaka Uba”) sunan nan Ibrahim, wanda ma’anarsa shi ne “Uban Jama’ar Al’ummai,” sa’ad da ya yi wa Abram alkawari cewa zai mai da shi “uban jama’ar al’ummai.” (Farawa 17:5) Hakazalika, Allah ya ba wannan dabbar sunan nan 666 don irin halayen da take da su.
Lambar nan shida tana wakiltar ajizanci. Sau da yawa akan yi amfani da lambobi a alamance a cikin Littafi Mai Tsarki. Bakwai tana wakiltar abin da ya cika ko kuma kamiltacce. Lambar nan shida ba ta kai bakwai ba, kuma hakan yana nufin abin da bai cika ba ko kuma abin da ke da lahani a gaban Allah. Irin yanayin da magabtan Allah suke ciki ke nan.—1 Labarbaru 20:6; Daniyel 3:1.
An rubuta lambar sau uku don a nuna muhimmanci. A wasu lokuta, idan ana so a nuna muhimmancin wani abu a cikin Littafi Mai Tsarki, akan ambata abin sau uku. (Ru’ya ta Yohanna 4:8; 8:13) Saboda haka, sunan nan 666 yana nuna yadda gwamnatocin da ’yan Adam suka kafa sun kasa sosai. Sun kasa kawo salama da kuma kwanciyar rai na dindindin ga ’yan Adam, abin da Mulkin Allah ne kadai zai iya cim ma.
Alamar dabbar
Littafi Mai Tsarki ya ce ana ba wa mutane alama ko “shaidar dabban” domin suna bin dabbar da “mamaki,” har ma su yi mata sujjada. (Ru’ya ta Yohanna 13:3, 4; 16:2) Sun mai da kasarsu kamar Allah domin sun fi daukaka ta kuma suna daukaka tutar kasarsu ko rundunarta.
Ta yaya ake rubuta wa mutum alamar dabbar a hannunsa ko a goshinsa? (Ru’ya ta Yohanna 13:16) Sa’ad da Allah ya ba wa al’ummar Isra’ila doka, ya ce musu: “Za ku daura su alama a hannuwanku, da goshinku.” (Kubawar Shari’a 11:18) Hakan ba ya nufin cewa Isra’ilawa za su rubuta dokar a hannunsu ko kuma a goshinsu, amma yana nufin cewa za su bar kalmomin su ja-goranci tunaninsu da dukan abubuwa da za su yi. Hakazalika, wannan lambar 666 ba lamba ce da ake rubuta a jikin mutane ba, amma hanya ce ta bayyana wadanda suke karkashin tsarin mulki da ’yan Adam suka kafa. Wadanda suke da alamar dabbar suna hamayya da Allah.—Ru’ya ta Yohanna 14:9, 10; 19:19-21.