Ta Yaya Yesu Ya Cece Mu?
Amsar Littafi Mai Tsarki
Yesu ya ceci mutane masu aminci sa’ad da ya ba da ransa. (Matiyu 20:28) Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya kira Yesu “Mai Ceton duniya.” (1 Yohanna 4:14) Littafi Mai Tsarki ya dada cewa: “Ba kuma samun ceto ga wani, gama cikin dukan sunayen da aka ba mutane a karkashin sama, ba wani suna dabam da aka bayar wanda lallai ta wurinsa ne za mu sami ceto.”—Ayyukan Manzanni 4:12.
Yesu “ya mutu saboda kowa” da ya ba da gaskiya gare shi. (Ibraniyawa 2:9; Yohanna 3:16) Bayan haka, “Allah ya tashe shi daga matattu” kuma Yesu ya koma sama a matsayin ruhu. (Ayyukan Manzanni 3:15) A wajen, Yesu “yana da iko, yau da kullum, ya ceci duk wadanda suke matsowa kusa da Allah ta wurinsa, tun da yake kullum a raye yake, domin ya yi roko ga Allah a madadinsu.”—Ibraniyawa 7:25.
Me ya sa muke bukatar Yesu ya yi roko a madadinmu?
Domin dukanmu masu zunubi ne. (Romawa 3:23) Zunubi yana nisanta mu daga Allah kuma hakan yana jawo mutuwa. (Romawa 6:23) Amma Yesu yana taimaka wa wadanda suka ba da gaskiya ga fansar da ya yi. (1 Yohanna 2:1) Yana roko a madadin su sa’ad da yake rokon Allah ya ji addu’o’insu kuma ya gafarta musu zunubansu ta wajen hadayarsa. (Matiyu 1:21; Romawa 8:34) Allah yana jin wadannan rokon da Yesu ya yi domin sun jitu da nufinsa. Shi ya sa Allah ya tura Yesu ya zo duniya “domin duniya ta sami ceto ta wurinsa.”—Yohanna 3:17.
Yin imani da Yesu ne kawai zai sa mu sami ceto?
A’a. Ban da yin imani da Yesu, da akwai wasu abubuwa da ya kamata mu yi don mu sami ceto. (Ayyukan Manzanni 16:30, 31) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kamar yadda jikin mutumin da ba shi da ruhu gawa ne, haka kuma bangaskiya marar ayyuka take daidai da gawa.” (Yaƙub 2:26) Don mu sami ceto, wajibi ne:
Mu koyi game da Yesu da Ubansa Jehobah.—Yohanna 17:3.
Mu karfafa bangaskiyarmu a gare su.—Yohanna 12:44; 14:1.
Mu nuna bangaskiyarmu ta wajen bin umurninsu. (Luka 6:46; 1 Yohanna 2:17) Yesu ya ce ba kowa ba ne da ke ce masa “Ubangiji” zai sami ceto amma wadanda suke ‘yin abin da Ubansa wanda yake cikin sama yake so.’—Matiyu 7:21.
Mu ci gaba da kasancewa da bangaskiya ko da muna shan wahala. Yesu ya nuna hakan sa’ad da ya ce: “Wanda ya jimre har zuwa ƙarshe, zai tsira.”—Matiyu 24:13.