Koma ka ga abin da ke ciki

SINGAPUR

An Kai Su Kurkuku Saboda Imaninsu

An Kai Su Kurkuku Saboda Imaninsu

Gwamnatin kasar Singafo tana tilasta wa mutane su yi aikin soja kuma ta ki ta amince cewa kowa na da ’yanci ya ki yin wani abu saboda imaninsa. Akan tsare matasa maza Shaidun Jehobah da suka ki su shiga soja a kurkuku har na tsawon watanni 39.

Idan wani Mashaidi matashi ya kai shekara 18, ana kiransa ya shiga soja bisa ga dokar sojoji na kasar. Idan ya ki yin hakan, za a tsare shi a sansanin sojoji har tsawon watanni 15. A karshen wannan lokacin, sai a gaya masa ya saka kayan soja don ya soma koyan aikin soja nan da nan. Idan ya ki, sai kotun soji ya sake yanke masa hukunci kuma a sake tsare shi na tsawon watanni 24.

Kasar Singafo Ta Ki Ta Bi Dokar MDD

Tun da dadewa, Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a cikin muhimmin jawabinta a kan Hakkokin ’Yan Adam cewa ya kamata duka mambobinta su amince cewa ’yan kasa suna da ’yancin kin shiga soja domin kowane dan Adam yana da “’yancin yin tunani da ’yancin bin lamirinsa da kuma addini.” Ko da yake kasar Singafo mambar Majalisar Dinkin Duniya ce tun shekara ta 1965, ta nuna rashin yarda da wannan matakin da MDD ta dauka a kan wannan batun. A cikin wasikar da wani ma’aikacin gwamnatin Singafo ya rubuta zuwa ga Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta MDD a ranar 24 ga Afrilu, 2002, ma’aikacin ya ce “a duk lokacin da imanin wani ya saba wa [hakkin kāre tsaron kasa], gwamnati tana da ’yanci ta daukaka tsaron kasa bisa ’yancin dan Adam.” Ma’aikacin ya kara da cewa: “Ba mu yarda da wannan umurni cewa kowace kasa ta daukaka ’yancin kowane dan Adam na kin shiga soja domin imaninsa ba.”

Jerin Shekaru

  1. 11 ga Yuni, 2015

    Shaidun Jehobah guda 18 ne aka tsare a kurkuku domin sun ki su shiga soja saboda imaninsu.

  2. 10 ga Maris, 2015

    An tsare Shaidun Jehobah guda 17 a kurkuku domin sun ki su shiga soja saboda imaninsu.

  3. 12 ga Disamba, 2014

    Shaidun Jehobah guda 19 ne aka tsare a kurkuku domin sun ki su shiga soja saboda imaninsu, hade da wani da ya ki ya zama sojan wucin gadi.

  4. 16 ga Satumba, 2014

    Shaidun Jehobah maza guda 15 ne aka tsare a kurkuku domin sun ki su shiga soja saboda imaninsu, hade da wani da ya ki ya zama sojan wucin gadi.

  5. 30 ga Yuli, 2014

    An tsare Shaidu guda 16 a barikin soja na Singafo, wato Singapore Armed Forces Detention Barracks domin sun ki su shiga soja saboda imaninsu.

  6. Nuwamba, 2013

    An tsare Shaidu guda 18 domin sun ki su shiga soja saboda imaninsu.

  7. 24 ga Afrilu, 2002

    Wani ma’aikacin gwamnati ya sanar cewa Singafo ba ta amince da ’yancin kin shiga soja saboda imani ba.

  8. Fabrairu, 1995

    Yadda ake tsananta wa Shaidun Jehobah a Singafo ya karu.

  9. 8 ga Agusta, 1994

    Babban Kotun Singafo ya yi banza da karar da Shaidun Jehobah suka daukaka.

  10. 12 ga Janairu, 1972

    Gwamnatin Singafo ta janye rajistar Shaidun Jehobah.