Koma ka ga abin da ke ciki

RASHA

An Saka Su a Fursuna Domin Imaninsu

An Saka Su a Fursuna Domin Imaninsu

A ranar 25 ga Mayu na shekara ta 2017, wasu ‘yan sanda rike da makamai da kuma wasu Hukumomin Tsaron kasar Rasha sun je inda Shaidun Jehobah suke ibadarsu a garin Oryol da ke kasar Rasha ba gaira ba dalili. Da yake tun a watan Yuni na shekara ta 2016 ne hukuma ta dakatar da ayyukan ibada na Shaidun Jehobah a duk fadin kasar domin tana zargi cewa su masu tsattsauran ra’ayi ne, yanzu suna da’awa cewa taron da suke yi ma na cikin ayyukan da suka saba wa dokar kasar.

Lauyar da ya shigar da karar ya yi kulli don a kama Mallam Dennis Christensen da laifi don ibadar da yake yi. Bawan Allahn nan dai dattijo ne a ikilisiyar Shaidun Jehobah da ke Oryol. Amma kotun yankin Sovietskiy da ke birnin Oryol, ta ce a ci gaba da tsare Malam Dennis Christensen har sai 23 ga Nuwamba na 2017, ta yi hakan ne domin a ba wa Hukumomin Tsaron kasar Rasha lokaci su yi bincike don su tabbatar da cewa yana da laifi kafin a kira Shaidun Jehobah a gaban kotu. Shaidun Jehobah sun shigar da kara a ranar 29 ga Mayu, 2017 don matakin da kotun ta dauka na ci gaba da tsare wannan bawan Allahn. Da suka je kotun a ranar 21 ga Yuni, 2017, kotun ta ki amince da bukatarsu kuma ta ce a ci gaba da tsare Malam Christensen. Kuma idan suka yanke hukuncin bisa shafi na 282.2, sashe na 1 na dokar kasar, Malam Christensen zai ci gaba da zama a fursuna har shekaru shida zuwa goma.

Nan da nan sai aka sanar da Ofishin Jakadancin kasar Denmark da ke Moscow cewa an kama dan kasarsu mai suna Malam Christensen dan kabilar Danish kuma an tura wakilai don su gana da shi a fursunan. Wakilan sun dawo da rahoto cewa ba a wulakanta shi ba kuma bai da wata matsala a fursunan.

Kotun Kolin Rasha Sun Yi Rashin Adalci A Hukuncin da Suka Yanke

Abin da ya sa aka dakatar da ibadar Shaidun Jehobah a Oryol shi ne, jami’ar tsaro sun je majami’ar Shaidun Jehobah kuma suka “gano” littattafan da suke bayyana Littafi Mai Tsarki da su jami’an tsaron da kansu suka boye a wurin. Me ya sa muka ce hakan? Domin Shaidun Jehobah ba su bar wani littafi a wurin ba tun lokacin da gwamnati ta ce littattafan sun saba wa doka. Lauyoyin sun nuna littattafai kadan da suka kawo wajen ba da hujja cewa a “wurin ne ake ajiye littattafan da doka ta hana kuma daga baya a rarraba wa mutane.” Da Shaidun Jehobah suka daukaka kara zuwa Kotun Kolin Rasha, sai ita ma ta goyi bayan kotun Oryol wajen kin barin Shaidun Jehobah su ci gaba da ibadarsu.

A watan Maris 2017, Ma’aikatar Shari’a a kasar Rasha ta kawo karar Ofishi da majami’un Shaidun Jehobah da ke kasar har da kuma wasu kananan addinai da ke kasar. Da aka yi shari’ar a ranar 20 ga Afrilu, 2017, sai Kotun Kolin Rasha ta dakatar da dukan ayyukan ibadar Shaidun Jehobah a kasar. Don haka, Shaidun Jehobah sun daukaka kara kuma ba su yarda cewa su “ ’yan tsattauran ra’ayi” ne ba amma masu ibada ne hankali kwance. Kamar yadda ya faru a Oryol, “tabbacin” da aka bayar a kotun kulli ne da jami’an tsaron suka yi kuma hakan ya saba wa doka. Ban da haka ma, “masanan” kotun da suka bincika littattafan ba su fahimci abin da littattafan suke fada ba.

Kokarce-Kokarce Don a Kāre ‘Yancin Addini

Sa’ad da Jami’an Tsaro suka je majami’ar da ke Oryol ba gaira ba dalili a ranar 25 ga mayu 2017, sun same su suna nazarin Littafi Mai Tsarki hankali kwance, ba wai suna goyon bayan wata kungiyar addini ba ne. Shaidun Jehobah za su ci gaba da daukaka kararraki a kasar Rasha kuma sun sanar da hukumomi a wasu kasashe game da Malam Dennis Christensen da kuma dukan Shaidun Jehobah da ke kasar Rasha.

Abubuwan da Suka Faru

  1. 21 ga Yuni, 2017

    Bayan da aka daukaka kara, kotun ta ce a ci gaba da rike Malam Dennis Christensen a fursuna.

  2. 26 ga Mayu, 2017

    Kotun ta yanke wa Dennis Christensen jiran shari’a na wata biyu.

  3. 25 ga Mayu, 2017

    An shiga majami’ar Shaidun Jehobah a Oryol kuma an kama Malam Dennis Christensen.