Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TAMBAYA TA 2

Me Ya Sa Nake Yawan Damuwa da Surar Jikina?

Me Ya Sa Nake Yawan Damuwa da Surar Jikina?

ABIN DA YA SA HAKAN YAKE DA MUHIMMANCI

Akwai abubuwan da suka fi abin da muke gani a cikin madubi muhimmanci.

MENE NE ZA KA YI?

Ka yi tunanin wannan yanayin: Sa’ad da Julia ta dubi kanta a madubi, sai ta ga cewa ta yi ƙiba sosai. Sai ta ce, “Ina bukatar in rage jiki,” duk da cewa iyayenta da abokanta sun gaya mata cewa ita “siririya ce kamar tsinke.”

Kwanan nan, Julia ta yi tunani sosai a kan yadda za ta rage jiki. Abin da za ta yi shi ne za ta yi ’yan kwanaki ba ta ci abinci ba . . .

Idan ka sami kanka a yanayin da Julia take ciki, mene ne za ka yi?

KA DAKATA KA YI TUNANI!

Ra’ayinka game da surarka zai iya zama kamar ganin siffarka a madubin da ya koɗe

Ba laifi ba ne mutum ya damu da surar jikinsa. Hakika, Littafi Mai Tsarki ya ambaci maza da mata masu kyan gaske, kamar Saratu da Rahila da Abigail da Yusufu da kuma Dauda. Littafi Mai Tsarki ya ce wata mata mai suna Abishag “kyakyawa ce ƙwarai.”—1 Sarakuna 1:4.

Amma, matasa da yawa suna yawan damuwa game da surar jikinsu. Hakan zai iya jawo matsaloli masu tsanani. Alal misali:

  • Wani bincike da aka yi a Amirka ya nuna cewa kashi 58 na ’yammata suna ganin cewa suna da ƙiba, amma a gaskiya, kashi 17 ne kawai suke da ƙiba sosai.

  • Wani bincike kuma a Amirka ya nuna cewa kashi 45 na mata da ba su da jiki sun ɗauka cewa suna da ƙiba sosai!

  • A garin neman rage ƙiba, wasu matasa suna kamuwa da cutar anorexia, wato cutar da ke kashe ƙwayoyin da ke riƙe abinci a ciki ta yadda ba za su iya sarrafa abincin ba balle su gina jiki.

Idan kana ganin kana da wannan cutar ko kuma wani yanayi da yake hana ka cin abinci, ka nemi taimako. Ka soma da gaya wa iyayenka ko kuma wani amininka da ba tsararka ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Aboki kullayaumi ƙauna yake yi, kuma an haifi ɗan’uwa domin kwanakin shan wuya.”—Misalai 17:17.

GYARA MAFI KYAU DA ZA KA IYA YI!

Hakika, halin mutum ne yake sa mutane su so shi ko kuma su ƙi shi. Dubi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Absalom, ɗan Sarki Dauda:

“Babu wanda ya isa yabo kamar Absalom ga zancen kyaun jiki. . . . Babu aibi a cikinsa.”—2 Sama’ila 14:25.

Duk da haka, wannan matashin yana da girman kai da dogon buri kuma shi mayaudari ne! Ƙari ga haka, Littafi Mai Tsarki bai kwatanta Absalom a matsayin mutumin kirki ba; maimakon haka, ya nuna cewa shi mugun munafuki ne da kuma maci amana.

Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ba mu wannan shawarar:

‘Ku yafa sabon mutum.’—Kolosiyawa 3:10.

“Kada adonku ya zama ado na waje, . . .  amma ya zama ɓoyayyen mutum na zuciya.”—1 Bitrus 3:3, 4.

Ko da yake yin ado ba laifi ba ne, amma halin mutum ya fi siffa muhimmanci. A ƙarshe, halin mutum ne zai sa mutane su so shi ba kyaunsa ba! Wata yarinya mai suna Phylicia ta ce: “Kyaun siffa yakan ja hankalin mutane, amma halayenka masu kyau ne za su sa mutane su so ka.”

KA YI LA’AKARI DA SURAR JIKINKA

Shin kana yawan fushi game da surar jikinka?

Shin ka taɓa yin tunanin yin shafe-shafe ko kuma ƙin cin abinci don ka daidaita wani aibi da kake da shi?

Idan so samu ne, mene ne za ka so ka canja game da surar jikinka? (Ka ja layi a ƙarƙashin waɗanda kake so.))

  • TSAYI

  • ƘIBA

  • GASHI

  • SURAR JIKI

  • FUSKA

  • LAUNIN FATA

Idan amsarka e ce ga tambayoyi biyu na farko kuma ka zaɓi abubuwa uku a tambaya ta uku, ka yi la’akari da wannan: Wataƙila mutane ba sa yi maka kallon mummuna kamar yadda kake yi wa kanka. Idan ba ka mai da hankali ba, za ka riƙa damuwa sosai game da surar jikinka kuma ka ɗauki matakan da za su wuce gona da iri.—1 Sama’ila 16:7.