Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TAMBAYA TA 4

Mene ne Ya Kamata In Yi Sa’ad da Na Yi Kuskure?

Mene ne Ya Kamata In Yi Sa’ad da Na Yi Kuskure?

ABIN DA YA SA HAKAN YAKE DA MUHIMMANCI

Idan ka amince da kurakuranka, hakan zai sa ka zama mai hankali kuma mutane za su yarda da kai.

MENE NE ZA KA YI?

Ka yi tunanin wannan yanayin: Sa’ad da Tim yake ƙwallo da abokansa, sai ya buga ƙwallon kuma ya fasa gilashin gaba na motar maƙwabcinsu.

Idan kai ne Tim, me za ka yi?

KA DAKATA KA YI TUNANI!

KANA DA ZAƁI UKU:

  1. Ka gudu.

  2. Ka ɗora wa wani laifin.

  3. Ka gaya wa maƙwabcinku abin da ya faru kuma ka ce za ka biya.

Wataƙila za ka so ka yi Zaɓi na ɗaya. Amma akwai dalilai da yawa da ya sa ya kamata ka amince da kurakuranka ko da ka fasa gilashin mota ne ko kuma wani abu dabam.

DALILAI UKU DA SUKA SA YA KAMATA KA AMINCE DA KURAKURANKA

  1. Abin da ya kamata ka yi ke nan.

    Littafi Mai Tsarki ya ce: “Muna kuwa so mu tafiyar da al’amuranmu da halin kirki.”—Ibraniyawa 13:18, Littafi Mai Tsarki.

  2. Mutane sukan gafarta wa waɗanda suka amince da kurakuransu.

    Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wanda ya rufe laifofinsa ba za ya yi albarka ba: Amma dukan wanda ya faɗe su ya kuwa rabu da su za ya sami jinƙai.”—Misalai 28:13.

  3. Mafi muhimmanci, yana faranta wa Allah rai.

    Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mashiririci [“mai ruɗu,” NW] abin ƙyama ne ga Ubangiji: Amma asirinsa yana tare da masu-adalci.”—Misalai 3:32.

A Amirka, wata yarinya ’yar shekara 20 mai suna Karina ta ki ta gaya wa mahaifinta cewa an ci ta tara saboda tsananin gudu da mota. Ta yi ƙoƙari ta ɓoye rasit ɗin don kada mahaifinta ya gani. Karina ta ce: “Bayan kusan shekara guda, mahaifina ya ga rasit ɗin. Hakan ya sa na shiga uku!”

Wane darasi ne ta koya? Karina ta ce: “Ɓoye kurakuran da ka yi yana sa abubuwa su ƙara muni. Daga baya, gaskiya za ta fito!”

KA KOYI DARASI DAGA KURAKURANKA

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dukanmu mukan yi tuntuɓe.” (Yaƙub 3:2) Amma kamar yadda muka gani, idan muka amince da kurakuran da muka yi nan da nan, hakan yana nuna cewa mu masu tawali’u ne kuma mun manyanta.

Wani abin da ya kamata ka yi shi ne ka koyi darasi daga kurakuranka. Wata yarinya mai suna Vera ta ce: “Ina ƙoƙarin koyan darasin da zai taimaka mini in zama mutumiyar kirki daga kowane kuskuren da na yi, da kuma yadda zan bi da yanayin idan hakan ya sake faruwa.” Bari mu ga yadda za ka iya yin hakan.

Ka fita yawo da babur ɗin mahaifinka, sai ka lalata shi. Me za ka yi?

  • Za ka yi shiru kuma kana fatan cewa kada mahaifinka ya gani.

  • Za ka gaya wa mahaifinka abin da ya faru.

  • Za ka gaya wa mahaifinka abin da ya faru amma ka ɗora wa wani laifin.

Ka faɗi jarrabawa don ba ka yi karatu ba. Me za ka yi?

  • Za ka ce jarabawar tana da wuya sosai.

  • Za ka amince da laifinka.

  • Za ka ce malaminka ba ya son ka.

Yin tunanin kurakuran da ka yi a dā, yana kama da kallon madubin ganin baya sa’ad da kake tuƙa mota

Yanzu ka duba waɗannan yanayin kuma ka ɗauka cewa kai ne (1) mahaifinka da kuma (2) malaminka. Mene ne mahaifinka da kuma malaminka za su ce idan ka amince da kurakuranka nan da nan? Da wane ido za su kalle ka idan ka ɓoye kurakuranka?

Yanzu ka yi tunani a kan kuskuren da ka yi shekarar da ta shige kuma ka amsa waɗannan tambayoyin.

Wane kuskure ne ka yi? Mene ne ka yi bayan hakan?

  • Na ɓoye laifin da na yi.

  • Na ɗora wa wani laifin.

  • Na amince da kuskurena nan da nan.

Idan ba ka amince da kuskurenka ba, yaya ka ji bayan haka?

  • Na ji daɗin cewa ba a ga kuskuren da na yi ba!

  • Zuciyata ta dame ni don ban faɗi gaskiya ba.

Wanne mataki mafi kyau ya kamata ka ɗauka?

Mene ne ka koya daga kuskurenka?

MENE NE RA’AYINKA?

Me ya sa wasu mutane ba sa amincewa da kurakuran da suka yi?

Yaya mutane za su riƙa kallon ka idan kana ɓoye kurakuranka a kowane lokaci? Amma, yaya za su riƙa kallon ka idan kana amincewa da kurakuranka?—Luka 16:10.