Ka Girmama Wanda Ya Cancanci Girmamawa
“Ga wanda yake zaune bisa kursiyin, ga Ɗan rago kuma, albarka, da daraja, da ɗaukaka, da mulki, har zuwa zamanun zamanai.”
WAƘOƘI: 9, 108
1. Me ya sa muke girmama wasu mutane, kuma mene ne za mu bincika yanzu?
GIRMAMA mutum yana nufin a riƙa daraja shi. Hakika, ana girmama mutum ne idan ya yi abin da ya cancanta ko kuma yana da wani matsayi na musamman. Saboda haka, ya kamata mu yi wannan tambayar, wane ne ya kamata mu girmama kuma me ya sa ya dace mu yi hakan?
2, 3. (a) Me ya sa ya dace mu girmama Jehobah? (Ka duba hoton da ke shafin nan.) (b) Wane ne Ɗan rago da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna 5:
2 Kamar yadda littafin Ru’ya ta Yohanna 5:13 ta nuna, “wanda yake zaune bisa kursiyin, . . . Ɗan rago” ya cancanci mu girmama shi. Kuma an ambata wani dalili a sura 4 na littafin da ya sa ya kamata mu girmama Jehobah. Halittu da ke sama suna yabon Jehobah, “wanda yake rayuwa har zuwa zamanun zamanai.” Halittun suna cewa: “Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.”
Yoh. 1:29) Littafi Mai Tsarki ya ce, ya fi dukan sarakuna a dā da kuma na yanzu. Wurin ya ce: ‘Sarkin sarakuna, Ubangijin iyayengiji; wanda ba ya mutuwa, mazauni cikin haske wanda ba shi kusantuwa; mutum ba ya taɓa ganinsa, ba kuwa mai-ikon ganinsa.’ (1 Tim. 6:
4. Me ya sa ya zama wajibi mu girmama Jehobah da kuma Kristi?
4 Wajibi ne mu girmama Jehobah da kuma Kristi. Don idan ba mu yi hakan ba, ba za mu sami rai na har abada ba. Yesu ya nuna mana hakan ta abin da ya faɗa a littafin Yohanna 5:
5. Me ya sa ya kamata mu riƙa girmama mutane kuma mu daraja su?
5 Allah ya halicci mutane a “kamaninsa.” (Far. 1:27) Saboda haka, yawancinsu suna nuna wasu halaye da Allah yake da su. Mutane suna iya nuna ƙauna ga juna, su yi wa juna alheri kuma su ji tausayin wasu. Tun da yake Allah ya halicce mu da waɗannan halaye, mun san abin da ya dace da abin da bai dace ba da kuma abin da ya kamata mu yi da wanda bai kamata mu yi ba. (Rom. 2:
YADDA YA KAMATA KA GIRMAMA MUTANE
6, 7. A batun girmama mutane, yaya Shaidun Jehobah suka bambanta da mutane da yawa?
6 Ya kamata mu mai da hankali don mu san irin girmamawar da za mu riƙa ba wa mutane. Halin duniyar Shaiɗan ne yake rinjayar yawancin mutane a yau. Shi ya sa mutane sukan bauta ma wasu maza ko mata maimakon su girmama su ko kuma su daraja su yadda ya kamata. Suna ɗaukaka shugabannin addinai da ‘yan siyasa da taurari ‘yan wasa da masu yin fina-finai da dai sauransu, kuma hakan yakan sa suna ɗaukan su a matsayin allansu. Shi ya sa manya da ƙanana suke yin koyi da su, wataƙila suna kwaikwayon yadda suke magana da kuma tufafinsu da halayensu.
7 Kiristoci na gaskiya suna da ra’ayin da ya dace game da ɗaukaka mutane. Kristi ne kaɗai mutumin da ya taɓa yin rayuwa a duniya da ya kafa kamiltaccen misalin da za mu bi. (1 Bit. 2:21) Allah ba zai yi farin ciki ba idan muna ɗaukaka mutane a hanyar da ba ta dace ba. Ya kamata mu riƙa tuna cewa: “Dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah.” (Rom. 3:23) Hakika, bai dace a ɗaukaka mutum fiye da kima ba har ya zama kamar ana bauta masa.
8, 9. (a) Ta yaya Shaidun Jehobah suke ɗaukan ma’aikatan gwamnati? (b) Yaya ya kamata mu girmama ma’aikatan gwamnati?
8 Akwai mutanen da suke riƙe da
9 Saboda haka, Shaidun Jehobah suna girmama irin waɗannan ma’aikatan gwamnati da son ransu, kamar yadda aka saba yi a ƙasarsu. Muna ba su haɗin kai yayin da suke aikinsu. Hakika, yadda muke girmama su da kuma tallafa musu yana da iyaka kamar yadda Nassosi suka ce. Ba za mu yi wa Allah rashin biyayya ba ko kuma mu ɓata dangantakarmu da Jehobah don kawai muna so mu yi wa gwamnati biyayya.
10. Ta yaya bayin Jehobah na dā suka kafa mana misali mai kyau a dangantakarsu da ma’aikatan gwamnati?
10 Bayin Jehobah a dā sun kafa mana misali mai kyau a dangantakarsu da ma’aikatan gwamnati. Yusufu da Maryamu sun yi biyayya a lokacin da Sarkin Roma ya ce mutanensa su koma gida don ana so a yi ƙirge. Sun yi tafiya zuwa Bai’talami duk da cewa Maryamu ta kusan haifan ɗanta na fari. (Luk. 2:
11, 12. (a) Me ya sa ba ma ba wa shugabannin addinai daraja na musamman? (b) Wane sakamako aka samu sa’ad da wani Mashaidi ɗan Austriya ya daraja wani ɗan siyasa?
11 Amma, Shaidun Jehobah ba sa bi da shugabannin addinai a matsayin waɗanda za a girmama fiye da yadda ya kamata ba, ko da yake suna son hakan. Addinan ƙarya suna ɓata sunan Allah kuma ba sa koyar da gaskiyar da ke cikin Kalmarsa. Saboda haka, muna daraja su yadda muke yi wa mutane, amma ba ma nuna musu daraja ta musamman. Yesu ya kira irin waɗannan mutanen a zamaninsa munafukai da makafin da suke ja-gora. (Mat. 23:
12 Alal misali, Leopold Engleitner Mashaidi ne mai ƙwazo daga Austriya. ‘Yan Nazi sun kama shi suka tura shi sansanin da ke Buchenwald a cikin jirgin ƙasa. Wani fursuna mai suna Dokta Heinrich Gleissner yana cikin jirgin. Shi ɗan siyasa ne a Austriya, amma ‘yan Nazi ba sa son shi. A kan hanyarsu ta zuwa sansanin, sai Ɗan’uwa Engleitner ya bayyana wa Gleissner abin da ya yi imani da shi kuma Gleissner ya saurara sosai. Bayan yaƙin duniya na biyu, Gleissner ya yi amfani da ikonsa don ya taimaka wa Shaidu da ke Austriya. Kana iya tuna da wasu sakamako masu kyau da aka samu sa’ad da Shaidu suka girmama ma’aikatan gwamnati yadda ya dace kuma suka daraja su yadda Littafi Mai Tsarki ya ce su yi.
WASU DA SUKA CANCANCI GIRMAMAWA
13. Su waye musamman suka dace mu riƙa girmama su, kuma me ya sa?
13 Ya kamata mu riƙa girmama waɗanda suke bauta wa Jehobah tare da mu, 1 Timotawus 5:17.) Muna girmama waɗannan ‘yan’uwan ko da daga wace ƙasa ce suka fito, kome yawa ko ƙanƙantar iliminsu, matsayinsu ko su talakawa ne ko kuma masu kuɗi. Littafi Mai Tsarki ya kira su “kyautai ga mutane” kuma Allah yana amfani da su don ya biya bukatun mutanensa. (Afis. 4:8) Waɗannan ‘yan’uwan su ne dattawan ikilisiya da masu kula da da’ira da Kwamitin da ke kula da ofishin Shaidun Jehobah da kuma Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. ‘Yan’uwan da ke ƙarni na farko sun girmama waɗanda suke ja-gora sosai, ya kamata mu ma mu yi hakan a yau. Ko da yake ba ma bauta wa waɗanda suke ja-gora a ikilisiya ko kuma mu riƙa yi musu kallon mala’iku. Duk da haka, muna girmama su kuma muna daraja su domin aiki tuƙuru da suke yi da kuma yadda suke da sauƙin kai.
14, 15. Ka nuna bambanci da ke tsakanin dattawa da shugabannan addinan ƙarya.
14 Waɗannan dattawan suna ƙarfafa ‘yan’uwansu. Saboda sauƙin kansu, ba sa bari mutane su bi da su kamar taurari. Ta yin hakan, sun bambanta da shugabannan addinai da yawa a yau da kuma na ƙarni na farko da Yesu ya ce: “Suna son mazaunai na manya cikin bukukuwa da mazauna na manya cikin majami’u, da gaisuwa kuma cikin kasuwanni.”
15 Dattawa masu tawali’u suna yin biyayya da kalamin Yesu cewa: “Kada a kira ku Malam: gama malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa ‘yan’uwa ne. Kuma kada ku ce da kowane mutum a duniya ubanku: gama ɗaya ne Ubanku, shi na sama. Kada kuwa a ce da ku iyayengiji: gama ɗaya ne Ubangijinku, Kristi. Amma wanda shi ke mafi girma a cikinku shi zama mai-hidimanku. Kuma dukan wanda za ya ɗaukaka kansa za ya ƙasƙanta; dukan wanda ya ƙasƙantar da kansa kuwa za ya ɗaukaka.” (Mat. 23:
16. Me ya sa ya kamata ka ci gaba da yin ƙoƙari don ka yi abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da girmama mutane yadda ya dace?
16 Hakika, zai ɗauki lokaci mu san yadda ya kamata mu riƙa girmama mutane da kuma wanda za mu yi wa hakan. Kiristoci na ƙarni na farko sun fuskanci A. M. 10:
ALBARKA DA ZA MU SAMU IDAN MUNA GIRMAMA MUTANE
17. Mene ne amfanin girmama hukuma?
17 Hukumomin za su kāre ‘yanci yin wa’azi da muke da shi idan muka girmama su kuma muka daraja su. Sau da yawa, hakan yana iya sa mutane su kasance da ra’ayin da ya dace game da wa’azin da muke yi. Alal misali, shekaru da yawa da suka shige, Birgit wata majagaba a Jamus ta halarci bikin sauke karatun ‘yarta. Malaman sun gaya mata cewa suna farin cikin koyar da yaran Shaidu. Sun ce zai zama abin kunya da a ce ba yaran Shaidu a makarantarsu. Sai Birgit ta bayyana musu cewa, “Muna koya wa yaranmu su bi ƙa’idodin Allah kuma hakan ya ƙunshi girmama da kuma daraja malamansu.” Wata malama ta ce, “Idan dukan yara suna yin abubuwa kamar yaranku, za a ji daɗin koyarwa sosai.” Bayan makonni da yawa, ɗaya daga cikin malaman ta halarci taron yanki a birnin Leipzig.
18, 19. Me ya sa ya kamata mu riƙa girmama dattawa a hanyar da ta dace?
18 Ya kamata ƙa’idodin da ke cikin Kalmar Allah su riƙa yi mana ja-gora idan muna girmama dattawa. (Karanta Ibraniyawa 13:
19 Muna taimaka wa dattawa idan muka girmama da kuma daraja su a hanyar da ta dace, ba tare da bi da su kamar taurari ba. Hakan zai taimaka musu su guji girman kai ko kuma tunanin sun iya abu fiye da wasu ko kuma sun fi kowa adalci.
20. Ta yaya girmama wasu yake taimaka mana?
20 Hakika, girmama mutane da suka cancanci girmamawa zai hana mu zama masu son kai. Zai taimaka mana mu guji zama masu girman kai idan muka sami wani gata. Ban da haka ma, zai sa mu riƙa bin umurnin ƙungiyar Jehobah, wadda take hana mu girmama ko ɗaukaka masu bi ko marasa bi a hanyar da ba ta dace ba. Ƙari ga haka, zai taimaka mana mu ci gaba da bauta wa Jehobah idan wasu da muke girmamawa suka yi abin da bai dace ba.
21. Waɗanne albarka muke samu idan muka girmama mutane da suka cancanta a hanyar da ta dace?
21 Wasu albarka kuma da za mu samu idan muna girmama mutanen da suka cancanta shi ne cewa muna faranta wa Allah rai. Muna yin abin da yake so kuma hakan zai taimaka mana mu riƙe amincinmu. Ban da haka ma, hakan zai sa Jehobah ya ba da amsa ga wanda yake zarginsa. (Mis. 27:11) Duniya tana cike da mutanen da ba su san yadda ya kamata a girmama mutane ba. Saboda haka, muna godiya don yadda ake koya mana mu girmama mutane a hanyar da ta dace.