Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Kasance da Tabbaci a Kan Alkawuran da Jehobah Ya Yi

Ka Kasance da Tabbaci a Kan Alkawuran da Jehobah Ya Yi

“Bangaskiya fa . . . tabbacin al’amuran da ba a gani ba tukuna.”​—IBRAN. 11:1.

WAƘOƘI: 54, 125

1. A matsayinmu na Kiristoci, yaya ya kamata mu ɗauki bangaskiyar da muke da shi?

BANGASKIYA hali ne mai tamani da Kiristoci suke da shi. Ba kowane ɗan Adam ne yake da bangaskiya ba. (2 Tas. 3:⁠2) Amma Jehobah ya ba wa dukan bayinsa “gwargwadon bangaskiya.” (Rom. 12:3; Gal. 5:22) Ya kamata mu yi godiya don bangaskiyar da muke da shi.

2, 3. (a) Waɗanne albarka ne mutumin da yake da bangaskiya zai iya samu? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna yanzu?

2 Yesu Kiristi ya ce Ubansa na sama yana amfani da Ɗansa don ya sa mutane su soma bauta masa. (Yoh. 6:​44, 65) Idan mutum ya gaskata da Yesu, hakan zai sa a iya gafarta masa zunubansa. Kuma hakan zai sa ya sami gatan ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah har abada. (Rom. 6:23) Shin mun cancanci samun wannan albarkar? Domin mu ajizai ne, ba mu cancanci samun kome ba sai mutuwa. (Zab. 103:10) Amma Jehobah ya ga cewa muna da amfani sosai. Domin yana ƙaunar mu, ya taimaka mana mu koyi abubuwa masu kyau game da Yesu da kuma fansar da ya ba da. Don haka muka soma gaskatawa da Yesu kuma muka samu begen rai na har abada.​—⁠Karanta 1 Yohanna 4:​9, 10.

3 Mece ce bangaskiya? Idan mun san abin da Allah yake mana yanzu da kuma wanda zai yi mana a nan gaba, shin hakan yana nufin cewa muna da bangaskiya? Mafi muhimmanci, a waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna cewa muna da bangaskiya?

‘KA BA DA GASKIYA A CIKIN ZUCIYARKA’

4. Ka bayyana dalilin da ya sa bangaskiya ba kawai sanin abin da Allah yake yi mana ba ne?

4 Kasancewa da bangaskiya ba sanin abin da Allah da kuma Yesu suka yi mana kawai ba ne. Amma tana motsa mu mu yi rayuwar da ta jitu da nufin Allah. Idan Kirista ya ba da gaskiya ga hanyar da Allah ya yi amfani da ita don ya ceci ‘yan Adam, hakan zai motsa shi ya yi wa mutane wa’azi. Manzo Bulus ya ce: ‘Gama idan ka shaida da bakinka Yesu Ubangiji ne, ka kuma ba da gaskiya cikin zuciyarka Allah ya tashe shi daga matattu, za ka tsira: gama da zuciya mutum yake ba da gaskiya zuwa adalci; da baki kuma ake shaida zuwa ceto.’​—⁠Rom. 10:​9, 10; 2 Kor. 4:⁠13.

5. Me ya sa bangaskiya take da muhimmanci sosai, kuma ta yaya za mu iya ƙarfafa ta? Ka ba da misali.

5 Don mu ji daɗin rayuwa a sabuwar duniya, muna bukatar mu kasance da kuma ƙarfafa bangaskiyarmu. Yin hakan yana kama da yin shuki. Shuka tana bukatar ruwa da kuma kulawa don ta yi girma. Amma idan ba ta samu isashen ruwa ba, hakan zai sa shukar ta mutu. Hakazalika, za mu iya daina kasancewa da bangaskiya idan ba ma yin abubuwan da za su ƙarfafa ta. (Luk. 22:32; Ibran. 3:12) Idan muna mai da hankali ga bangaskiyarmu, za ta yi ƙarfi da kuma “girma ƙwarai.” Ƙari ga haka, za mu zama “sahihai cikin bangaskiya.”​—⁠2 Tas. 1:3; Tit. 2:2.

YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA BAYYANA MA’ANAR BANGASKIYA

6. A waɗanne hanyoyi biyu ne littafin Ibraniyawa 11:1 ta bayyana ma’anar bangaskiya?

6 Littafin Ibraniyawa 11:1 ta bayyana abin da bangaskiya take nufi. (Karanta.) Bangaskiya ta ƙunshi abubuwa gudu biyu da ba za mu iya gani da idanunmu ba: (1) Bangaskiya ita ce “ainihin abin da muke begensa.” Hakan ya ƙunshi alkawuran da Allah ya yi game da nan gaba. Alal misali, muna da tabbaci cewa za a kawo ƙarshen mugunta kuma za a mai da duniyar nan aljanna. (2) Bangaskiya ita ce “tabbacin al’amuran da ba a gani ba tukuna.” Alal misali, mun gaskata da Allah da Yesu Kristi da mala’iku da kuma Mulkin Allah a sama duk da cewa ba ma ganin su. (Ibran. 11:⁠3) Ta yaya za mu nuna cewa muna da bangaskiya kuma mun gaskata da abubuwan da ke cikin Littafi Mai Tsarki? Za mu iya nuna hakan ta kalamanmu da kuma ayyukanmu. Idan ba haka ba, bangaskiyarmu matacciya ce.

7. Ta yaya misalin Nuhu ya taimaka mana mu fahimci abin da yake nufi mutum ya kasance da bangaskiya? (Ka duba hoton da ke shafi na 26.)

7 Littafin Ibraniyawa 11:7 ta ambata irin bangaskiyar Nuhu ya kasance da shi sa’ad da ta ce: ‘Da aka faɗakar da shi a kan al’amuran da ba a gani ba tukuna, domin tsoro mai-ibada, sai ya shirya jirgi domin ceton gidansa.’ Ta wurin gina babban jirgin, Nuhu ya nuna cewa yana da bangaskiya. Babu shakka, maƙwabtansa za su tambaye shi me ya sa yake gina wannan babban jirgin. Shin Nuhu ya yi shiru ne ko kuma ya ce musu ina ruwansu? A’a! Bangaskiyar Nuhu ta motsa shi ya gaya musu game da hukuncin da Allah zai yi wa ‘yan Adam, kuma ya yi hakan da gaba gaɗi. Wataƙila Nuhu ya sāke maimaita musu abin da Jehobah ya gaya masa cewa: “Na riga na yi niyyar hallaka dukan talikai, gama duniya tana cike da ayyukansu na zunubi . . . zan kawo rigyawa bisa duniya, ta hallaka dukan mai numfashin rai da yake ƙarkashin sama, dukan abin da yake a duniya zai mutu.” Ƙari ga haka, Nuhu ya bayyana wa mutanen abin da suke bukatar su yi don su tsira kuma ya ce dole ne su “shiga cikin jirgi.” Ta haka, Nuhu ya ƙara nuna cewa yana da bangaskiya domin ya zama “mai-shelan adalci.”​—⁠Far. 6:​13, 17, 18, Littafi Mai Tsarki; 2 Bit. 2:⁠5.

8. Mene ne Yaƙub ya ce game da bangaskiya?

8 Wataƙila Yaƙub ya rubuta wasiƙarsa ba da daɗewa ba bayan manzo Bulus ya rubuta nasa bayanin game da bangaskiya. Kamar Bulus, Yaƙub ya bayyana cewa Kiristoci suna nuna bangaskiyarsu ta ayyukansu. Shi ya sa ya ce: “Ka nuna mini bangaskiyarka ba tare da ayyuka ba, ni kuwa ta wurin ayyukana in nuna maka bangaskiyata.” (Yaƙ. 2:18) Yaƙub ya nuna bambancin da ke tsakanin gaskatawa da kuma kasancewa da bangaskiya. Alal misali, aljanu sun gaskata cewa akwai Allah amma ba su da bangaskiya. Suna yin abubuwan da suka saɓa wa nufin Allah. (Yaƙ. 2:​19, 20) Amma mutumin da yake da bangaskiya yana yin abubuwan da suke faranta wa Allah rai. Abin da Ibrahim ya yi ke nan, shi ya sa Yaƙub ya ce: “Ko ba ta wurin ayuka ubanmu Ibrahim ya barata ba, yayin da ya miƙa Ishaƙu ɗansa bisa bagadi? Ka gani fa bangaskiya ta aika tare da ayukansa, ta wurin ayuka kuma bangaskiya ta cika.” Don a fahimci wannan batun, Yaƙub ya daɗa cewa: “Kamar yadda jiki ba tare da ruhu ba matacce ne, haka nan kuma bangaskiya ba tare da ayyuka ba matacciya ce.”​—⁠Yaƙ. 2:​21-23, 26.

9, 10. Mene ne gaskatawa da Yesu ya ƙunsa?

9 Fiye da shekara talatin bayan haka, manzo Yohanna ya rubuta Linjilarsa da kuma wasiƙa guda uku. Kamar sauran marubutan Littafi Mai Tsarki, shi ma ya fahimci abin da bangaskiya take nufi. A yawancin rubutunsa, Yohanna ya yi amfani da kalmar Helenanci nan da aka fassara zuwa “ba da gaskiya.”

10 Alal misali, Yohanna ya ce: “Wanda yana ba da gaskiya ga Ɗan yana da rai na har abada; amma wanda bai ba da gaskiya ga Ɗan ba, ba zai gan rai ba, amma fushin Allah yana bisansa zaune.” (Yoh. 3:36) Don haka, bangaskiya ta ƙunshi yin biyyaya ga umurnin Yesu. A yawancin lokaci, Yohanna ya ambata kalaman Yesu da suka nuna cewa mutum yana bukatar ya ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarsa.​—⁠Yoh. 3:16; 6:​29, 40; 11:​25, 26; 14:​1, 12.

11. Ta yaya za mu nuna godiya don yadda Jehobah ya sa muka san gaskiya game da shi da kuma Ɗansa?

11 Ya kamata mu nuna godiya don yadda Jehobah yake amfani da ruhunsa mai tsarki don ya koya mana game da shi da Ɗansa kuma ya taimaka mana mu kasance da bangaskiya. (Karanta Luka 10:21.) Muna bukatar mu ci gaba da gode wa Jehobah don yadda ya yi amfani da Ɗansa “shugaban bangaskiyarmu da mai-cikanta” don mu iya soma bauta masa. (Ibran. 12:2) Ya kamata mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu ta wurin yin addu’a da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki. Idan muka yi hakan, muna nuna godiya don abubuwan da Jehobah ya yi mana.​—Afis. 6:18; 1 Bit. 2:2.

Ka nuna bangaskiyarka ta wurin yin amfani da kowace dama don ka yi wa’azi game da Mulkin Allah (Ka duba sakin layi na 12)

12. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna cewa muna da bangaskiya?

12 Ya kamata mu ci gaba kasancewa da tabbacin cewa Allah zai cika alkawuransa. Kuma wajibi ne mu nuna hakan ta ayyukanmu. Alal misali, mu ci gaba da yin wa’azi game da Mulkin Allah da kuma taimaka wa mutane su soma bauta masa. Ƙari ga haka, mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu wajen “aika nagarta zuwa ga dukan mutane, tun ba waɗanda suke cikin iyalin imani ba.” (Gal. 6:10) Kuma mu yi ƙoƙari don mu “tuɓe tsohon mutum tare da ayyukansa,” da kuma guje wa duk wani abin da zai ɓata dangantakarmu da Jehobah.​—Kol. 3:​5, 8-10.

YIN IMANI DA ALLAH YANA DA MUHIMMANCI SOSAI

13. Me ya sa “bangaskiya ga Allah” take da muhimmanci? Ta yaya aka kwatanta hakan a cikin Littafi Mai Tsarki, kuma me ya sa?

13 Littafi Mai Tsarki ya ce, “Ba ya kuwa yiwuwa a gamshe shi ba sai tare da bangaskiya: gama mai-zuwa wurin Allah dole ya ba da gaskiya cewan yana da rai, kuma shi mai-sākawa ne ga dukan waɗanda ke biɗarsa.” (Ibran. 11:⁠6) Kalmar Allah ta ce “bangaskiya ga Allah” kamar “tushe” ce a gare mu, wato tana cikin abubuwa na farko da Kiristoci na gaskiya suke bukatar su kasance da shi. (Ibran. 6:⁠1) Amma ban da bangaskiya, da akwai wasu halaye da Kiristoci suke bukatar su kasance da shi don su “tsare [kansu] cikin ƙaunar Allah.”​—Karanta 2 Bitrus 1:​5-7; Yahu. 20, 21.

14, 15. Me ya sa ƙauna ta fi bangaskiya muhimmanci?

14 Marubutan Littafi Mai Tsarki sun ambata bangaskiya sau da yawa, kuma hakan ya nuna cewa bangaskiya tana da muhimmanci sosai. Babu wasu haleyen Kiristoci da aka ambata sosai kamar bangaskiya. Amma hakan ba ya nufin cewa bangaskiya ce hali mafi muhimmanci da Kiristoci suke bukatar su kasance da shi.

15 Bulus ya kwatanta bangaskiya da ƙauna kuma ya ce: “Idan ina da bangaskiya duka kuma, har da zan cira duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba komi ba ne.” (1 Kor. 13:⁠2) Amsar da Yesu ya bayar ga tambayar nan, “Wace ce babbar doka a cikin Attaurat?” ya nuna cewa ƙaunar Allah ce abu mafi muhimmanci. (Mat. 22:​35-40) Ƙauna tana taimaka mana mu kasance da wasu halaye har da bangaskiya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ƙauna . . . tana gaskata abu duka.” Ƙauna tana sa mu gaskata da abubuwan da Allah ya faɗa a cikin Littafi Mai Tsarki.​—⁠1 Kor. 13:​4, 7.

16, 17. Ta yaya aka ambata bangaskiya da kuma ƙauna tare a cikin Littafi Mai Tsarki, wanne ne ya fi muhimmanci kuma me ya sa?

16 Bangaskiya da ƙauna suna da muhimmanci sosai, shi ya sa a yawancin lokaci marubutan Littafi Mai Tsarki suna ambata waɗannan halayen tare ko kuma a jumla. Bulus ya ƙarfafa ‘yan’uwansa cewa su ‘yafe da sulke na bangaskiya da ƙauna.’ (1 Tas. 5:⁠8) Bitrus ya ce: ‘Ko da yake ba ku taɓa ganin [Yesu] ba, kuna ƙaunarsa. Ko da yake ba kwa ganinsa a yanzu, duk da haka kuna gaskatawa da shi.’ (1 Bit. 1:​8, LMT) Yaƙub ya gaya wa ‘yan’uwansa shafaffu cewa: ‘Ko Allah bai zaɓi fakirai ga wajen duniya su zama mawadata cikin bangaskiya ba, da magadan Mulki wanda ya alkawarta ga waɗanda suke ƙaunarsa?’ (Yaƙ. 2:⁠5) Bulus ya ce: “Ka kiyaye kwatancin sahihiyan kalmomi waɗanda ka ji daga gareni, cikin bangaskiya da ƙauna wadda ke cikin Kristi Yesu.”​—⁠2 Tim. 1:⁠13.

17 Ko da yake bangaskiya tana da muhimmanci sosai, amma za mu daina kasancewa da wannan halin sa’ad da muka ga cewa Allah ya cika alkawuransa kuma abubuwan da muke begensu sun faru. Amma ba za mu daina ƙaunar Allah da kuma maƙwabtanmu ba. Shi ya sa Bulus ya ce: “Yanzu dai bangaskiya, da bege, da ƙauna sun tabbata, su uku; amma mafi girmansu ƙauna ce.”​—⁠1 Kor. 13:⁠13.

JEHOBAH YA ALBARKACE MU DON MUN KASANCE DA BANGASKIYA

18, 19. Mene ne ya faru domin mutanen Allah sun kasance da bangaskiya a yau, kuma wane ne ya cancanci a yaba masa?

18 A zamaninmu, bayin Jehobah sun gaskata da Mulkin Allah. Suna ƙaunar juna sosai domin suna barin ruhu Allah ya yi musu ja-gora a rayuwarsu. Mene ne sakamakon hakan? ‘Yan’uwa maza da mata fiye da miliyan takwas a dukan faɗin duniya sun kasance da salama da kuma haɗin kai. (Gal. 5:​22, 23) Babu shakka, Jehobah ya albarkace mu don mun kasance da bangaskiya da kuma ƙauna!

19 Da taimakon Jehobah ne muka kasance da irin wannan haɗin kan. Ya cancanci mu yaba masa. Wannan aikin da muke yi yana sa a ɗaukaka ‘sunan Ubangiji, madawamiyar alama wadda ba za a datse ba.’ (Isha. 55:13) Hakika, “kyauta ce ta Allah” cewa an ‘an cece mu ta wurin bangaskiya.’ (Afis. 2:⁠8) Za mu ci gaba da kasancewa da salama da kuma haɗin kai har sai lokacin da dukan duniya za ta cika da kamiltattun mutane, masu aldaci da kuma farin ciki, waɗanda za su yabi Jehobah har abada. Bari mu ci gaba da kasancewa da tabbaci a kan alkawuran Jehobah!