Ta Yaya Mahaliccinmu Ya Bayyana Mana Abin da Zai Yi?
Tun lokacin da Allah ya halicci mutane, ya soma magana da su ta wurin mala’iku da kuma annabawa. Ƙari ga haka, ya sa an rubuta saƙonsa ga ’yan Adam da kuma alkawuran da ya yi musu. Allah ya gaya mana cewa za mu iya yin farin ciki a nan gaba. To, a ina ne za ka ga alkawuran da Allah ya yi mana a yau?
A cikin Nassosi Masu Tsarki ne aka rubuta alkawuran Allah. (2 Timoti 3:16) Ta yaya Allah ya sa annabawa su rubuta saƙonsa? (2 Bitrus 1:21) Allah ya taimaka musu su san saƙon ta hanyar mu’ujiza, sa’an nan suka rubuta shi. Za mu iya kwatanta shi da abin da manyan ’yan kasuwa sukan yi a yau. Idan ɗan kasuwa yana so ya aika saƙo, yakan sa sakatarensa ya rubuta masa saƙon. Ko da yake sakataren ne ya rubuta, saƙon na ɗan kasuwan ne. Hakazalika, duk da cewa Allah ya yi amfani da mutane su rubuta saƙon da ke cikin Nassosi Masu Tsarki, saƙon da ke ciki nasa ne.
AKWAI NASSOSI MASU TSARKI A KO’INA
Saƙon da Allah ya turo mana yana da amfani sosai, shi ya sa Allah ya tabbata cewa “kowace al’umma, da zuriya da yare,” sun same saƙon. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 14:6) Ana samun Nassosi Masu Tsarki, gabaki ɗayansu ko rabinsu a yaruka fiye da 3,000. Allah ne ya sa hakan ya yiwu. Babu wani littafin da aka fassara zuwa yaruka da yawa haka a duniya.