Zai Yiwu Ka More Albarkun Allah Har Abada
Allah ya yi wa annabi Ibrahim alkawari cewa wani daga zuriyarsa zai sa “dukan ƙabilun duniya” su sami albarka. (Farawa 22:18) Wane ne Allah ya zaɓa?
Kusan shekaru 2,000 da suka shige, Allah ya ba Yesu Almasihu ikon yin mu’ujizai, kuma shi daga zuriyar annabi Ibrahim ne. Mu’ujizan nan sun nuna cewa ta wurin Almasihu ne Allah zai cika alkawarin da ya yi wa annabi Ibrahim.—Galatiyawa 3:14.
Mu’ujizan sun kuma nuna cewa Almasihu ne wanda Allah ya zaɓa don ya yi wa dukan mutane albarka. Ƙari ga haka, abubuwan da Almasihu ya yi sun nuna irin alherin da Allah zai yi wa ’yan Adam a nan gaba. Ga misalin mu’ujizan da Almasihu ya yi, da suka nuna cewa yana da halayen kirki.
Almasihu mai alheri ne—Ya warkar da marasa lafiya.
Akwai lokacin da wani kuturu ya roƙi Almasihu ya warkar da shi. Sai Yesu Almasihu ya taɓa shi kuma ya ce: “Na yarda.” Nan tāke, mutumin ya warke.—Markus 1:40-42.
Almasihu mai bayarwa ne—Ya ciyar da mutanen da suke jin yunwa.
Yesu Almasihu bai ji daɗi ba da ya ga mutane suna jin yunwa. Fiye da sau ɗaya, Yesu ya yi amfani da ƙananan kifaye da burodi kaɗan, ya ciyar da dubban mutane. (Matiyu 14:17-21; 15:32-38) Kowa ya ci ya ƙoshi, har an sami raguwar abincin sosai. Wannan ba ƙaramin mu’ujiza ba ce!
Almasihu mai tausayi ne—Ya tā da wani mutumin da ya mutu.
Yesu Almasihu “ya ji tausayin” wata gwauruwa da take kukan rasuwar ɗanta. Yesu ya tā da yaron don ya san gwauruwar ba ta da wanda zai kula da ita.—Luka 7:12-15.