Yadda Za Mu Taimaka wa Yaran “Baki”
“Ba abin da ya fi faranta mini rai kamar in ji ’ya’yana suna bin gaskiya.”—3 YOH. 4, Littafi Mai Tsarki.
WAƘOƘI: 88, 41
1, 2. (a) Wace matsala ce yaran ’yan gudun hijira suke fuskanta? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika a wannan talifin?
JOSHUA wanda iyayensa ’yan gudun hijira ne ya ce: “Tun da aka haife ni, yarenmu nake yi a gida da kuma a ikilisiyarmu. Amma da na soma zuwa makaranta, sai na soma son yaren da ake yi a yankin. Bayan wasu shekaru, sai na daina yarenmu, idan na je taro ba na fahimtar abin da ake cewa, balle al’adarmu.” Yara da yawa suna fuskantar irin abin da Joshua ya fuskanta.
2 A yau, mutane fiye da miliyan 240 suna zama a wasu ƙasashe. Idan ka ƙauro daga wata ƙasa kuma kana da yara, ta yaya za ka taimaka wa yaranka su zama abokan Jehobah don su san ‘gaskiyar’ da ke cikin Littafi Mai Tsarki? (3 Yoh. 4) Kuma ta yaya wasu za su taimaka musu?
IYAYE KU KAFA MISALI MAI KYAU
3, 4. (a) Ta yaya iyaye za su kafa wa yaransu misali mai kyau? (b) Wane irin ra’ayi ne ya kamata iyaye su guji?
3 Misalin da iyaye suke kafa wa yaransu zai taimaka musu su bi hanyar rai. Yayin da yaranku suka ga cewa kuna “biɗan” mulkin Allah farko, hakan zai taimaka musu su koyi yadda za su riƙa dogara ga Jehobah don biyan bukatunsu. (Mat. 6:33, 34) Don haka, kuna bukatar ku sauƙaƙa rayuwarku kuma kada ku bar kayan duniya ya hana ku ibada. Ku yi ƙoƙari ku guji cin bashi. Ku nemo “wadata a sama,” wato tagomashin Jehobah ba dukiya ko “son girma wurin mutane” ba.—Karanta Markus 10:21, 22; Yoh. 12:43.
4 Bai kamata ka shagala da aiki ainun har ka kasa samun lokacin kasancewa da yaranka ba. Ka nuna musu cewa kana farin ciki da su sa’ad da suka saka Jehobah farko a rayuwarsu, maimakon nema wa kansu ko iyayensu dukiya ko suna. Ban da haka ma, ka guji ra’ayin nan cewa yara ne ya kamata su riƙa yi wa iyayensu tanadi. Littafi Mai Tsarki ya faɗa mana cewa “ba aikin ’ya’ya ba ne su yi tattalin iyaye, amma iyaye su yi ma ’ya’ya.”—2 Kor. 12:14.
IYAYE KU YI AMFANI DA YAREN DA YARANKU SUKE FAHIMTA
5. Me ya sa iyaye suke bukata su riƙa koya wa yaransu game da Jehobah?
5 Kamar yadda aka annabta, mutane daga “dukan harsunan al’ummai” za su zo su bauta wa Jehobah. (Zak. 8:23) Amma rashin iya wani yare zai sa ya yi maka wuya ka koya wa yaranka gaskiya game da Jehobah. Yaranka sune ɗalibanka da suka fi muhimmanci, saboda idan ka taimaka musu “su san” Jehobah, hakan zai sa su sami rai na har abada. (Yoh. 17:3) Ƙari ga haka, kafin yaranka su koya game da Jehobah, kana bukata ka ‘riƙa faɗin’ abubuwa game da shi a kai a kai.—Karanta Kubawar Shari’a 6:6, 7.
6. Ta yaya yara za su amfana daga koyan yaren iyayensu? (Ka duba hoton da ke shafi na 8.)
6 Babu shakka, yaranka za su iya koyan yaren da ake yi a makarantarsu da inda kuke zama, amma kafin su koyi yarenku kana bukata ka riƙa yi musu yaren a kai a kai. Koya wa yara yarenku zai taimaka musu su riƙa faɗa maka abin da yake damunsu, ban da haka, zai taimaka musu sosai. Idan yaranka sun iya wani yare za su amfana kuma su riƙa fahimtar ra’ayin wasu. Ƙari ga haka, zai ba su damar yi wa mutane wa’azi. Carolina wadda iyayenta sun zo daga wata ƙasa ta ce: “Ina jin daɗin ikilisiyar da ake wani yare, musamman ma don taimakawa a yin wa’azi a inda ake bukatar masu shela.”
7. Mene ne za ka yi don ka taimaka wa iyalinka?
7 A lokacin da yaran mutane da suka ƙauro daga wata ƙasa suka fara koyan yare da al’adar ƙasar da suke zama, wasun su ba za su so yarensu kuma ba. Idan haka yaranku suke, shin za ku yi ƙoƙari don ku koyi wasu daga cikin yarukan da ake yi a ƙasar da kuke? Idan kuka fahimci abin da suke faɗa da nishaɗin da suke so da kuma ayyukan makaranta da ake ba su kuma kuka iya yi wa malamansu magana, hakan zai taimaka muku ku yi renon yaranku da kyau. Ƙari ga haka, koyan wani yare yakan ɗauki lokaci da ƙwazo sosai da kuma kasancewa da tawali’u. Idan yaronka kurma ne, shin ba za ka koyi yaren kurame ba ne don ka riƙa yi masa magana? Haka yake da yaran da ba su iya yaren iyayensu ba, suna bukatar a yi musu hakan, ko ba haka ba? *
8. Ta yaya za ka taimaka wa yaranka idan ba ka iya yarensu sosai ba?
8 A gaskiya, zai iya yi wa iyaye wuya su koyi yaren da yaransu suke yi. Don haka, yakan yi musu wuya su koya wa yaransu gaskiyar da ke cikin “littattafai masu-tsarki” sosai. (2 Tim. 3:15) Idan kana cikin irin wannan yanayin, har ila za ka iya koya wa yaranka game da Jehobah kuma su ƙaunace shi. Wani dattijo mai suna Shan, ya ce: “Mahaifiyarmu ba ta iya yaren da muke yi sosai ba, kuma ni da ’yan’uwana mata ba mu iya yarenta sosai ba, amma da muka ga cewa tana iya ƙoƙarinta don yin nazarin Littafi Mai Tsarki da addu’a da ibada ta iyali kowane mako, hakan ya sa mun fahimci cewa sanin Jehobah yana da muhimmanci sosai.”
9. Ta yaya iyaye za su taimaka wa yara da suke bukatar su riƙa yin nazari a yare biyu?
9 Wasu yara suna bukatar su koya game da Jehobah a yare biyu, wato yaren da suke yi a makaranta da kuma yaren da suke yi a gida. Saboda haka, wasu iyaye suna yin amfani da littattafai da waɗanda aka ɗauka a tef da kuma bidiyoyi a yaruka biyun da yaransu suke ji. Hakika, iyayen da suka fito daga wata ƙasa suna bukatar su keɓe lokaci kuma su nuna cewa suna son su taimaka wa yaransu su ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah.
IKILISIYAR WANE YARE YA KAMATA KA RIƘA ZUWA?
10. (a) Wane ne yake da hakkin zaɓan taron da ya kamata iyali su halarta? (b) Mene ne ya kamata ya yi kafin ya tsai da shawara?
10 Idan “baƙi” ba sa kusa da Shaidun da suke yarensu, suna bukatar su riƙa halartar taro a yaren da ake yi a yankin. (Zab. 146:9) Amma idan akwai ikilisiyar da ake yin yarenka kuma fa? Kana bukatar ka tambayi kanka, shin a taron wane yare ne iyalina za su fi amfana? Magidanci yana bukatar ya yi addu’a da kuma tunani sosai, bayan haka, sai ya tattauna batun da matarsa da kuma yaransa kafin ya tsai da shawara. (1 Kor. 11:3) Mene ne magidanta suke bukatar su yi la’akari da shi? Wane ƙa’idodi suke bukatar su bi? Bari mu bincika.
11, 12. (a) Ta yaya yare yake shafan yadda yara suke koyan abu a taro? (b) Me ya sa wasu yara suke ƙin koyan yaren iyayensu?
11 Iyaye suna bukata su san bukatun yaransu sosai. Babu shakka, ko da wane yare ne suke yi, kafin yara su ƙulla dangantaka da Jehobah, zai dace iyaye su riƙa neman lokaci sosai domin su koyar da yarensu ba kawai abubuwan da suke ji a taronmu ba. Ka yi la’akari da wannan: Idan yara suka halarci taro a yaren da suke ji da kyau, ba zai musu wuya su fahimci abin da ake faɗa ba wataƙila za su koyi abubuwa fiye da yadda iyayensu suke zato. Amma hakan ba zai yiwu ba idan yara ba su fahimci yaren sosai ba. (Karanta 1 Korintiyawa 14:9, 11.) Kuma ba dole ba ne yaren iyayen ya zama yaren da yara suka fi fahimta. Wasu yara za su iya yin kalamai ko kuma yin gwaji ko ba da jawabi, idan suna zuwa taron ikilisiyar da ake yin yaren iyayensu, amma wataƙila ba daga zuciyarsu suke yin hakan ba.
12 Ban da haka ma, ba yaren ne kaɗai yake ratsa zuciyar yara ba. Abin da Joshua wanda aka ambata ɗazu ya ce ke nan. ’Yar’uwarsa Esther ta ce, “al’ada da yare da kuma addinin da iyaye suke bi suna shafan yaransu sosai.” Idan yara ba su fahimci al’adar iyayensu ba, hakan zai iya hana su son koyan yaren iyayensu da kuma imaninsu. Mene ne iyaye da suka ƙaura zuwa wata ƙasa za su yi?
13, 14. (a) Me ya sa wasu suka tsai da shawarar ƙaurar da iyalinsu zuwa ikilisiyar da ake yin yaren yankin? (b) Kuma ta yaya iyayen suka ci gaba da ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah?
13 Iyaye suna bukatar su taimaka wa yaransu su ƙulla dangantaka da Jehobah, ko da yin hakan ba zai yi musu sauƙi ba. (1 Kor. 10:24) Mahaifin Joshua da Esther mai suna Samuel ya ce, “Ni da matata mun gano cewa yaranmu ba sa fahimtar yarenmu sosai, bayan hakan, sai muka yi addu’a ga Jehobah don ya taimaka mana. Kuma mun ga cewa abin da zai magance wannan matsalar shi ne ƙaura zuwa ikilisiyar da ake yaren da mutanen garin suke yi, amma hakan bai da sauƙi ko kaɗan. Duk da haka, sai muka ƙaura zuwa ikilisiyar. Yanzu muna fita wa’azi kuma muna halartar taron tare, ban da haka ma, mukan gayyaci ’yan’uwa daga ikilisiyar don mu ci abinci tare kuma mu shaƙata. Yin irin waɗannan abubuwan sun taimaka wa yaranmu su san ’yan’uwan kuma su sa Jehobah ya zama uba da kuma abokinsu. A gare mu hakan ya fi muhimmanci fiye da koyan yarenmu.”
14 Samuel ya ƙara da cewa: “Don mu ma mu ci gaba da zama abokan Jehobah, ni da matata mukan halarci taro a yarenmu. Ko da yake yin haka yana da wuya, mun gode wa Jehobah don ya taimaka mana kuma ya albarkaci sadaukarwar da muka yi. Yanzu, yaranmu uku suna bauta wa Jehobah kuma suna yin hidima ta cikakken lokaci.”
ABIN DA MATASA ZA SU IYA YI
15. Me ya sa wata ’yar’uwa mai suna Kristina ta ga cewa ya kamata ta ƙaura zuwa ikilisiyar yaren da ta fi fahimta?
15 Matasa suna iya fahimtar cewa suna bukata su ƙaura zuwa ikilisiyar da ake yin yaren da suka fi fahimta don su bauta wa Jehobah. Idan suka yi hakan, bai kamata iyaye su ji cewa yaransu ba sa ƙaunar su ba. Kristina ta ce: “Na san wasu abubuwa a yaren iyayena, amma abin da ake faɗa a taron ba na fahimta. Da na kai shekara 12, na halarci taron yanki a yaren da ake yi a garin da muke zama, kuma wannan ne lokaci na farko da na fahimci cewa, lallai abin da ake koya mini gaskiya ne! Wani abu ma da ya taimaka mini shi ne lokacin da na fara yin addu’a a yaren da na koya a makaranta, don hakan ya sa ina yi wa Jehobah magana da dukan zuciyata.” (A. M. 2:11, 41) Sa’ad da Kristina ta zama matashiya ta tattauna batun komawa ikilisiyar yaren da ta fi fahimta da iyayenta kuma ta ƙaura zuwa ikilisiyar. Ta ƙara da cewa: “Da na koya game da Jehobah a yaren da na fi fahimta, hakan ya sa na ɗauki mataki.” Nan ba da daɗewa ba, sai Kristina ta fara yin hidimar majagaba ta cikakken lokaci.
16. Me ya sa wata ’yar’uwa mai suna Nadia ta yi farin cikin kasancewa a ikilisiyar da ake yaren iyayenta?
16 Matasa, shin kuna ganin kuna bukatar ku ƙaura zuwa ikilisiyar yaren da kuka fi fahimta? Idan haka ne, kana bukatar ka tambayi kanka, me ya sa? Shin ƙaura zuwa ikilisiyar zai taimaka maka ka daɗa ƙarfafa dangantakarka da Jehobah? (Yaƙ. 4:8) Shin za ka so ka ƙaura ne don ba ka so a riƙa sa maka ido ko don ba ka son aiki da yawa? Nadia wadda yanzu tana hidima a Bethel ta ce: “A lokacin da ni da ’yan’uwana muka zama matasa, mun so mu ƙaura zuwa ikilisiyar yaren da ake yi a wurin da muke zama.” Amma iyayenta sun san cewa idan suka bar yaransu suka ƙaura, yaran ba za su ci gaba da ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah ba. Nadia ta ƙara da cewa: “Muna gode wa iyayenmu da ba su bar mu mun ƙaura zuwa ikilisiya wani yare ba, amma sun yi iya ƙoƙarinsu don su koya mana yarensu, kuma hakan ya taimaka mana mu ci gaba da kasancewa a ikilisiyarsu. Ban da haka ma, ya taimaka mana mu sami damar koya ma wasu game da Jehobah.”
YADDA WASU ZA SU IYA TAIMAKAWA
17. (a) Wane ne Jehobah ya ba wa hakkin renon yara? (b) Ta yaya iyaye za su nemi taimako a kan yadda za su riƙa koyar da yaransu?
17 Jehobah ya ba wa iyaye hakkin renon yaransu da kuma koya musu game da shi, ba kakanni ko wasu ba. (Karanta Misalai 1:8; 31:10, 27, 28.) Duk da haka, iyayen da ba sa jin yaren da yaransu suke yi suna iya neman taimako don su san hanyoyin da za su tarbiyyartar da yaransu yadda ya dace. Amma idan suka nemi taimakon wasu ’yan’uwa don su koyar da yaransu, bai kamata su bar wa ’yan’uwan hakkin renon yaran ba. A maimakon haka, yin wannan hanya ɗaya ce da iyaye suke ‘tarbiyyar’ da kuma gargaɗar da yaransu ta “hanyar Ubangiji.” (Afis. 6:4, LMT) Alal misali, iyaye suna iya neman shawara daga dattawa a ikilisiya a kan yadda za su riƙa yin ibada ta iyali da kuma taimaka wa yaransu su san irin waɗanda ya kamata su yi abokantaka da su.
18, 19. (a) Ta yaya ’yan’uwan da suke ibada sosai za su iya taimaka wa yara? (b) Mene ne iyaye suke bukatar su yi?
18 Alal misali, a wasu lokuta iyaye suna iya gayyatar wasu iyalai don su yi ibada ta iyali tare. Ban da haka ma, matasa da yawa suna samun ci gaba idan suna fita wa’azi ko shaƙatawa da mutanen da suke da dangantaka mai kyau da Jehobah. (Mis. 27:17) Wani ɗan’uwa mai suna Shan, da aka ambata ɗazu ya ce: “Na tuna da ’yan’uwan da suka taimaka mini idan ina da jawabi, a duk lokacin da suka yi hakan, ina koyan abubuwa da yawa. Ƙari ga haka, ina jin daɗin shaƙatawar da muke yi tare.”
19 Babu shakka, waɗanda iyaye suka zaɓa don su taimakawa yaransu, suna bukatar su taimaka wa yaran su riƙa daraja iyayensu ta wajen faɗin abubuwa masu kyau game da iyayen. Ƙari ga haka, bai kamata su ƙwace hakkin renon yara daga wurin iyayensu ba. Ban da haka ma, waɗanda suke taimaka wa yaran suna bukatar su guji duk wani abun da zai iya sa mutane su soma zarginsu da yin abin da bai dace ba. (1 Bit. 2:12) Bai kamata iyaye su ba wasu hakkin tarbiyyartar da yaransu ba, amma idan ya zama dole sai wasu sun taimaka, iyayen suna bukatar su riƙa lura da yadda mutanen suke yin hakan da yake hakkin iyayen ne su tarbiyyartar da yaransu.
20. Ta yaya iyaye za su taimaka wa yaransu su riƙa bauta wa Jehobah da kyau?
20 Iyaye, ku yi wa Jehobah addu’a don ya taimaka muku ku yi iya ƙoƙarinku don renon yaranku. (Karanta 2 Labarbaru 15:7.) Abu mafi muhimmanci a gare ku shi ne taimaka wa yaranku su zama abokan Jehobah. Don haka, ku yi iya ƙoƙarinku don ku tabbatar da cewa Kalmar Allah tana ratsa zuciyar yaranku. Kada ku yi tunanin cewa yaranku ba za su ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah ba. Sa’ad da yaranku suke bin ƙa’idodin Kalmar Allah da kuma misalai masu kyau da kuka kafa musu, za ku yi farin ciki kuma ku ji kamar yadda manzo Yohanna ya ji da ya ce: “Ba abin da ya fi faranta mini rai kamar in ji ’ya’yana suna bin gaskiya.”—3 Yoh. 4.
^ sakin layi na 7 Ka duba talifin nan “You Can Learn Another Language!” a mujallar Awake! na watan Maris 2007, shafuffuka na 10-12.