Ka Yi Bimbini a Kan Kaunar Jehobah Marar Iyaka
“Zan yi ta bimbinin dukan aikinka.”—ZAB. 77:12.
WAƘOƘI:18, 61
1, 2. (a) Me ya sa kake da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mutanensa? (b) Wace bukata ce Allah ya sa a cikin zuciyar ’yan Adam?
MENE NE ya sa kake da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunar mutanensa? Kafin ka ba da amsa, ka yi la’akari da waɗannan misalan: Shekaru da yawa, ’yan’uwa sun ƙarfafa wata ’yar’uwa mai suna Taylene ta kasance da ra’ayin da ya dace kuma kada ta riƙa kafa maƙasudan da suka fi ƙarfinta. Ta ce: “Idan Jehobah ba ya so na, da bai zai ci-gaba da ba ni shawara a kai a kai ba.” Wata ’yar’uwa mai suna Brigitte da ta yi renon yaranta biyu bayan da mijinta ya rasu ta ce: “Kula da yara a wannan zamanin ba shi da sauƙi, musamman ga gwauraye. Amma na tabbata cewa Jehobah yana ƙaunata domin ya yi mini ja-gora a dukan matsaloli da na fuskanta, kuma bai bar ni na fuskanci yanayin da ya fi ƙarfina ba.” (1 Kor. 10:13) Wata ’yar’uwa mai suna Sandra tana fama da ciwon da ba shi da magani. A wani taron yanki da aka yi, wata matar wani ɗan’uwa ta nuna mata ƙauna. Mijin Sandra ya ce: “Ko da yake ba mu san ta sosai ba, yadda ta nuna cewa ta damu da mu ya sa mu farin ciki. Ƙaunar da ’yan’uwa suka nuna mana ko da kaɗan ne, ya nuna mini cewa Jehobah yana ƙaunarmu sosai.”
Isha. 41:13; 49:15.
2 Jehobah ya halicci ’yan Adam a yadda za su nuna ƙauna kuma a ƙaunace su. Amma, wasu abubuwa kamar ɓacin rai ko rashin lafiya ko rashin kuɗi ko kuma rashin sakamako masu kyau a wa’azi, za su iya sa mu ɗauka cewa Jehobah ba ya ƙaunarmu kuma. Idan muka soma irin wannan tunanin, zai dace mu tuna cewa muna da daraja a gabansa kuma yana ‘riƙe da hannun damarmu’ don ya taimaka mana. Ba zai taɓa manta da mu ba idan muna da aminci a gare shi.—3. Mene ne zai sa mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunarmu da gaske?
3 Mutanen da aka ambata ɗazu sun tabbata cewa Allah yana tare da su a mawuyacin lokaci. Mu ma za mu iya kasancewa da tabbaci cewa yana tare da mu. (Zab. 118:6, 7) A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa huɗu da suka nuna cewa Jehobah yana ƙaunarmu. Waɗannan abubuwa sune (1) abubuwan da ya halitta, (2) kalmarsa da ya hure, (3) addu’a, da kuma (4) fansa. Yin bimbini a kan abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi zai sa mu ƙara gode masa saboda ƙaunarsa a gare mu.—Karanta Zabura 77:11, 12.
KA YI BIMBINI A KAN HALITTUN JEHOBAH
4. Mene ne yin bimbini a kan abubuwan da Jehobah ya halitta ya koya mana?
4 Muna ganin tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunarmu a abubuwan da ya halitta. (Rom. 1:20) Alal misali, ya halicci wannan duniyar da mahalli da kuma yanayin da zai sa mu ji daɗin zama a cikinta. Ya ba mu kome da muke bukata don mu ji daɗin rayuwa. Yana ba mu abinci don mu ci-gaba da rayuwa. Jehobah ya halicci duniya a yadda za ta ba da amfanin gona da shuke-shuke dabam-dabam don mu iya dafa abinci masu daɗi da su, kuma hakan ya sa muna jin daɗin cin abinci. (M. Wa. 9:7) Wata ’yar’uwa mai suna Catherine tana jin daɗin kallon halittun Jehobah, musamman a watan Afrilu a ƙasar Kanada. Ta ce: “Ganin yadda aka tsara fure su tsira da kuma yadda tsuntsaye suke dawowa daga inda suka je cin rani, da yadda wani ƙaramin tsuntsu da ake kira hummingbird da ke zuwa kiwo a wurin da nake ajiye musu abinci a tagar kicin ɗina yana da ban sha’awa. Babu shakka, Jehobah yana ƙaunarmu, shi ya sa ya ba mu waɗannan abubuwa masu ban sha’awa.” Ubanmu na sama mai ƙauna yana jin daɗin abubuwan da ya halitta, kuma yana so mu ma mu ji daɗinsu.—A. M. 14:16, 17.
5. Ta yaya yadda Jehobah ya halicci ’yan Adam ya nuna yana ƙaunarsu?
5 Jehobah ya halicce mu a yadda za mu iya yin aiki mai kyau kuma mu ji daɗinsa. (M. Wa. 2:24) Nufinsa shi ne ’yan Adam su mamaye duniya, su mallake ta, su yi mulkin kifaye da tsuntsaye da kuma kowane abu mai rai. (Far. 1:26-28) Kuma Jehobah ya halicce mu da halaye masu kyau da za su taimaka mana mu yi koyi da shi!—Afis. 5:1.
KA ƊAUKI KALMAR ALLAH DA TAMANI
6. Me ya sa ya kamata mu nuna godiya don Kalmar Allah?
6 Jehobah ya ba mu Littafi Mai Tsarki domin yana ƙaunarmu. Littafi Mai Tsarki ya koya mana abin da muke bukatar mu sani game da Allah da kuma yadda ya yi sha’ani da ’yan Adam. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana yadda ya bi da Isra’ilawa da suka yi masa rashin biyayya a kai a kai. Zabura 78:38 ta ce: “Yana cike da tausayi, ya gafarta laifinsu, ba ya halaka su ba: i, sau dayawa fushinsa ya kan juya, ba ya zuga dukan hasalarsa ba.” Yin bimbini a kan wannan ayar zai taimaka mana mu fahimci yadda Jehobah yake ƙaunarmu da kuma kula da mu. Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana ƙaunarka.—Karanta 1 Bitrus 5:6, 7.
7. Me ya sa za mu ɗauki Littafi Mai Tsarki da tamani?
7 Allah yana mana magana ta wurin Littafi Mai Tsarki, saboda haka ya kamata mu ɗauke shi da tamani sosai. Idan iyaye da yaransu suna tattaunawa da kyau, hakan yana sa su so juna sosai kuma su riƙa amincewa da juna. Jehobah kuma fa? Ko da yake ba mu taɓa ganinsa ko kuma ji muryarsa ba, yana ba mu umurni ta wurin Kalmarsa. Muna bukatar mu ci-gaba da bin umurninsa. (Isha. 30:20, 21) Sa’ad da muka karanta Kalmar Allah, za mu san Jehobah kuma mu dogara a gare shi, domin shi ne yake mana ja-gora da kuma kāre mu.—Karanta Zabura 19:7-11; Misalai 1:33.
8, 9. Mene ne Jehobah yake so mu sani? Ka ba da misali daga cikin Littafi Mai Tsarki.
8 Jehobah yana son mu san cewa yana ƙaunarmu kuma yana mai da hankali ga halayenmu masu kyau, ba ga ajizancinmu ba. (2 Laba. 16:9) Alal misali, ya yi hakan da Sarki Jehoshaphat na Yahuda. A wani lokaci, Jehoshaphat ya tsai da shawara da ba ta dace ba. Ya amince ya bi Sarki Ahab na Isra’ila zuwa yaƙi da Suriyawa don su ƙwato Ramoth-gilead. Ko da yake annabawan ƙarya 400 sun tabbatar wa Ahab cewa zai ci nasara, Micaiah annabin Jehobah ya gaya masa cewa za a ci su a yaƙin. Ahab ya mutu a yaƙin kuma da ƙyar Jehoshaphat ya tsira. Bayan yaƙin, Jehobah ya yi amfani da Jehu ɗan Hanani ya tsauta wa Jehoshaphat. Duk da haka, ya ce masa, yana da wasu halayen “kirki.”—2 Laba. 18:4, 5, 18-22, 33, 34; 19:1-3.
9 A lokacin da Jehoshaphat ya soma sarauta, ya gaya wa hakimai da Lawiyawa da kuma firistoci su yi tafiya zuwa dukan biranen Yahuda don su koya wa mutanen Dokar Jehobah. Sun yi nasara sosai, har mutanen al’umman da ke kusa suka soma girmama Jehobah. (2 Laba. 17:3-10) Duk da cewa Jehoshaphat ya yi wauta, Jehobah bai manta da abubuwa masu kyau da ya yi ba. Wannan labarin Littafi Mai Tsarki ya nuna mana cewa ko da mu ajizai ne, Jehobah zai ci-gaba da ƙaunarmu idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu bauta masa da zuciya ɗaya.
KADA KA YI WASA DA GATAN YIN ADDU’A
10, 11. (a) Me ya sa addu’a kyauta ce ta musamman daga wurin Jehobah? (b) Ta waɗanne hanyoyi ne Allah zai iya amsa addu’o’inmu? (Ka duba hoton da ke shafi na 9.)
10 Uba mai ƙaunar yaransa yana sauraronsu da kyau sa’ad da suke son su yi magana da shi. Yana so ya san damuwansu da matsalolinsu don yana ƙaunarsu. Jehobah, Ubanmu da ke sama yana sauraronmu sa’ad da muke masa magana ta wurin yin addu’a.
11 Muna iya yin addu’a ga Jehobah a kowane lokaci. Shi abokinmu ne, kuma yana a shirye ya saurare mu a koyaushe. Taylene da aka ambata ɗazu ta ce: “Kana iya gaya masa duk abin da ke zuciyarka.” Sa’ad da muka gaya wa Allah abin da ke zuciyarmu, yana iya amsa mana ta wurin wani nassin Littafi Mai Tsarki ko talifi da ke cikin mujallarmu ko kuma ƙarfafa daga wani ɗan’uwa. Jehobah yana jin roƙe-roƙenmu kuma yana fahimtarmu ko da wasu ba su fahimci yanayinmu ba. Wannan tabbaci ne cewa Allah yana ƙaunarmu sosai.
12. Me ya sa ya kamata mu yi nazarin addu’o’i da ke cikin Littafi Mai Tsarki? Ka ba da misali.
12 Za mu iya koyan darussa masu muhimmanci daga addu’o’i da ke cikin Littafi Mai Tsarki. A wani lokaci, zai dace mu yi nazarin irin waɗannan addu’o’in sa’ad da muke ibada ta iyali. Za mu kyautata addu’o’inmu, sa’ad da muka yi bimbini a kan yadda bayin Jehobah a dā suka gaya masa matsalolinsu. Alal misali, ka yi la’akari da addu’ar da Yunana ya yi da tawali’u sa’ad da yake cikin babban kifi. (Yun. 1:17–2:10) Ka yi bitar addu’ar da Sulemanu ya yi da zuciya ɗaya ga Jehobah a lokacin da aka keɓe haikali. (1 Sar. 8:22-53) Ka yi bimbini a kan addu’ar misali da Yesu ya yi don mu amfana. (Mat. 6:9-13) Mafi muhimmanci ma, “ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah” a kai a kai. A sakamako, “salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku da tunaninku.” Kuma hakan zai sa mu ci-gaba da nuna godiya ga Jehobah saboda yadda yake ƙaunarmu.—Filib. 4:6, 7.
KA NUNA GODIYA DON TANADIN FANSA
13. Wace dama ce ’yan Adam suka samu domin fansa?
13 Jehobah ya ba mu kyautar fansa “domin mu rayu.” (1 Yoh. 4:9) Da manzo Bulus yake magana game da wannan ƙauna mafifici da Allah ya nuna mana, ya ce: “Kristi ya mutu domin marasa-ibada. Gama da ƙyar wani za ya yarda ya mutu sabili da mutum mai-adalci; wataƙila dai sabili da nagarin mutum wani ya yi ƙarfin hali har shi mutu. Amma Allah yana shaidar ƙaunarsa garemu, da yake, tun muna masu-zunubi tukuna, Kristi ya mutu sabili da mu.” (Rom. 5:6-8) Wannan mafificin ƙauna da Jehobah ya nuna wa ’yan Adam ta sa sun sami damar ƙulla dangantaka na kud da kud da shi.
14, 15. Mene ne fansa take nufi ga (a) Kiristoci shafaffu? (b) waɗanda suke da begen zama a duniya?
14 A wata hanya ta musamman, Jehobah ya nuna ƙauna ga wani ƙaramin rukuni na Kiristoci. (Yoh. 1:12, 13; 3:5-7) Da yake an shafa waɗannan da ruhu mai tsarki, sun zama “’ya’yan Allah.” (Rom. 8:15, 16) Bulus ya ce waɗannan Kiristoci shafaffu an ‘tashe su tare da shi cikin sammai.’ (Afis. 2:6) Sun sami wannan matsayin domin an yi musu ‘hatimi da ruhu mai tsarki na alkawari wanda shi ne tabbacin gādonsu,’ wato “begen da ke cikin sama” da aka ajiye dominsu.—Afis. 1:13, 14; Kol. 1:5.
15 Yawancin ’yan Adam da suka ba da gaskiya ga fansa za su samu gatan zama abokan Jehobah. Ƙari ga haka, zai ɗauke su a matsayin ’ya’yansa kuma za su yi rayuwa har abada a cikin Aljanna a duniya da ya yi musu alkawarinsa. Saboda haka, tanadin fansa da Jehobah ya yi ya nuna cewa yana ƙaunar dukan ’yan Adam. (Yoh. 3:16) Idan muna da begen yin rayuwa a duniya har abada kuma muka ci-gaba da bauta wa Jehobah da aminci, za mu kasance da tabbaci cewa Allah zai sa mu ji daɗin rayuwa a sabuwar duniya. Saboda haka, mu nuna cewa muna godiya don fansa, wadda ta nuna cewa ƙaunar Allah a gare mu ba ta da iyaka!
KA ƘAUNACI JEHOBAH
16. Yin bimbini a kan hanyoyi da yawa da Jehobah ya nuna yana ƙaunarmu zai motsa mu mu yi me?
16 Jehobah ya nuna mana ƙauna a hanyoyi da yawa kuma ba za mu iya ambata duka ba. Sarki Dauda ya ce: “Ina misalin darajar tunaninka zuwa gareni, ya Allah! Ina misalin yawan jimlarsu! Idan zan ƙididdige su, sun fi yashi yawa.” (Zab. 139:17, 18) Yin bimbini a kan hanyoyi masu yawa da Jehobah ya nuna yana ƙaunarmu zai sa mu ƙaunace shi kuma mu bauta masa da dukan zuciyarmu.
17, 18. Waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna cewa muna ƙaunar Allah?
17 Da akwai hanyoyi da yawa da za mu nuna muna ƙaunar Jehobah. Alal misali, muna ƙaunar Allah da kuma maƙwabtanmu ta wajen yin wa’azin Mulki da himma. (Mat. 24:14; 28:19, 20) Muna nuna cewa muna ƙaunar Jehobah da gaske ta wajen jimre gwajin da muke fuskanta a matsayinmu na masu aminci. (Karanta Zabura 84:11; Yaƙub 1:2-5.) Ko da gwajin da muke fuskanta yana da tsanani, muna da tabbaci cewa Allah ya san wahalar da muke sha kuma zai taimaka mana, don muna da tamani a gare shi.—Zab. 56:8.
18 Ƙaunarmu ga Jehobah za ta sa mu yi bimbini a kan abubuwan da ya halitta da kuma ayyukansa. Idan muna nazarin Littafi Mai Tsarki da ƙwazo, hakan zai nuna muna ƙaunar Allah da kuma daraja Kalmarsa. Ƙaunar Jehobah za ta sa mu kusace shi ta yin addu’a. Kuma muna ƙara ƙaunar Allah sosai yayin da muka yi bimbini a kan hadayar fansa da ya yi tanadinsa don zunubanmu. (1 Yoh. 2:1, 2) Waɗannan ne wasu cikin dalilai da yawa da muke da su na nuna wa Jehobah cewa muna godiya saboda ƙaunarsa marar iyaka.