Kana “Kaunar Makwabcinka Kamar Ranka” Kuwa?
“Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.”—MAT. 22:39.
WAƘOƘI: 73, 36
1, 2. Ta yaya Nassosi ya nuna cewa ƙauna tana da muhimmanci?
ƘAUNA ita ce halin Jehobah na musamman. (1 Yoh. 4:16) Yesu ne Jehobah ya fara halitta. Ya yi shekaru aru-aru yana zama tare da Jehobah a sama kuma a wannan lokacin, ya lura da yadda Jehobah yake nuna ƙaunarsa ga halittunsa. (Kol. 1:15) Kamar Jehobah, Yesu ya nuna ƙauna sa’ad da yake sama da kuma a lokacin da ya zo duniya. Saboda haka, mun tabbata cewa Jehobah da Yesu za su ci gaba da yin sarauta cikin ƙauna har abada.
2 Sa’ad da wani mutum ya tambayi Yesu dokar da ta fi muhimmanci a cikin Attaura, Yesu ya ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka. Wannan ce babbar doka, ita ce kuwa ta fari. Wata kuma ta biyu mai kamaninta ita ce, Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.”—Mat. 22:37-39.
3. Su wane ne ‘maƙwabtanmu’?
3 Ka lura cewa bayan ƙaunar Allah, dokar da ta fi muhimmanci ita ce ƙaunar maƙwabci. Hakan ya nuna cewa ƙauna tana da muhimmanci a dukan cuɗanya da muke yi. Amma, su
wane ne ‘maƙwabtanmu’? Idan muna da aure, maƙwabcinmu ko maƙwabciyarmu ta farko ita ce abokiyar aurenmu. ’Yan’uwanmu masu bi maƙwabtanmu ne har ila. Ƙari ga haka, mutanen da muke yi musu wa’azi ma maƙwabtanmu ne. Da yake mu bayin Jehobah ne da kuma almajiran Yesu, ta yaya ya kamata mu ƙaunaci maƙwabtanmu?MA’AURATA, KU ƘAUNACI JUNA
4. Mene ne zai taimaka wa ma’aurata su jin daɗin aurensu duk da cewa mu ajizai ne, kuma me ya sa?
4 Jehobah ya halicci Adamu da Hawwa’u kuma ya haɗa su a matsayin mata da miji. Wannan shi ne aure na farko. Nufinsa shi ne su zauna tare, su yi farin ciki kuma cika duniya da ’ya’yansu. (Far. 1:27, 28) Amma, sa’ad da suka yi rashin biyayya ga Jehobah, hakan ya ɓata aurensu kuma ya hadassa zunubi da kuma mutuwa ga dukan ’yan Adam. (Rom. 5:12) Duk da haka, ma’aurata za su iya jin daɗin aurensu idan suka bi umurnin da ke cikin Littafi Mai Tsarki game da aure. Da yake Jehobah ne ya ba da waɗannan umurnin kuma shi ne tushen aure, ma’aurata za su yi nasara idan suka bi.—Karanta 2 Timotawus 3:16, 17.
5. Me ya sa ƙauna take da muhimmanci a aure?
5 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa so da ƙauna za su sa mu ji daɗin cuɗanya da muke yi da mutane kuma hakan gaskiya ne, musamman ma a aure. Sa’ad da manzo Bulus yake kwatanta ƙauna ta gaskiya, ya ce: “Ƙauna tana da yawan haƙuri, tana da nasiha; ƙauna ba ta jin kishi; ƙauna ba ta yin fahariya, ba ta yin kumbura, ba ta yin rashin hankali, ba ta biɗa ma kanta, ba ta jin cakuna, ba ta yin nukura, ba ta yin murna cikin rashin adalci, amma tana murna da gaskiya; tana jimrewa da abu duka, tana gaskata abu duka, tana kafa bege ga abu duka, tana daurewa da abu duka. Ƙauna ba ta ƙarewa daɗai.” (1 Kor. 13:4-8) Idan ma’aurata suka yi bimbini a kan waɗannan kalaman kuma suka bi su, za su kyautata zaman aurensu.
6, 7. (a) Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da shugabanci? (b) Ta yaya ya kamata Kirista ya bi da matarsa?
6 Jehobah ne ya ba da umurni cewa 1 Kor. 11:3) A nan, ba a ce miji ya mulki matarsa ko ya wulaƙanta ta ba. Alal misali, Jehobah shi ne shugaban Kristi, amma ya nuna masa alheri da ƙauna. Yesu ya ji daɗin yadda Allah yake yi masa ja-gora shi ya sa ya ce: “Ina ƙaunar Uba.” (Yoh. 14:31) Da a ce Jehobah ya bi da Yesu kamar mai mulkin kama-karya, da Yesu bai faɗi hakan ba.
namiji ya zama shugaban iyali kuma hakan ya nuna cewa ƙauna tana da muhimmanci a aure. Manzo Bulus ya ce: “Ina so ku sani, kan kowane namiji Kristi ne; kan mace kuma namiji ne; kan Kristi kuma Allah ne.” (7 Miji shi ne shugaban matarsa, amma Littafi Mai Tsarki ya umurce shi ya “girmama” ta. (1 Bit. 3:7, Littafi Mai Tsarki) Wata hanya da mazaje za su iya yin hakan ita ce ta yin la’akari da bukatun matansu da kuma ta ba su fifiko a wasu batutuwa. Kalmar Allah ta ce: “Ku mazaje, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kristi kuma ya ƙaunaci ikilisiya, ya ba da kansa domin ta.” (Afis. 5:25) Hakika, Yesu ya sadaukar da ransa a madadin mabiyansa. Idan miji ya bi gurbin Yesu, zai kasance da sauƙi wa matarsa ta daraja shi, ta so shi kuma ta yi masa biyayya.—Karanta Titus 2:3-5.
KA SO ’YAN’UWANKA MASU BI
8. Yaya ya kamata masu bauta wa Jehobah su ɗauki ’yan’uwansu masu bi?
8 A yau, miliyoyin mutane a faɗin duniya suna bauta wa Jehobah kuma suna sanar da mutane game da sunansa da kuma nufinsa. Yaya ya kamata Mashaidin Jehobah ya ɗauki ɗan’uwansa mai bi? Kalmar Allah ta ba da amsar: “Bari mu aika nagarta zuwa ga dukan mutane, tun ba waɗanda suke cikin iyalin imani ba.” (Gal. 6:10; karanta Romawa 12:10.) Manzo Bitrus ya rubuta cewa: “Da ya ke kun tsarkake rayukanku cikin biyayyarku ga gaskiya zuwa ga sahihiyar ƙauna ta ’yan’uwa, sai ku yi ƙaunar junanku daga zuciya mai-gaskiya.” Ya daɗa da cewa: “Gaba da kome kuma ku zama da ƙauna mai-huruwa zuwa ga junanku.”—1 Bit. 1:22; 4:8.
9, 10. Me ya sa mutanen Allah suke da haɗin kai a tsakaninsu?
9 Shaidun Jehobah sun fita dabam a faɗin duniya. Me ya sa? Don muna ƙaunar ’yan’uwanmu masu bi daga zuciyarmu. Ƙari ga haka, Jehobah yana tanadar mana da ruhu mai tsarki don muna ƙaunarsa kuma muna bin dokokinsa. Hakan yana taimaka mana mu kasance da haɗin kai a duk inda muke a faɗin duniya.—Karanta 1 Yohanna 4:20, 21.
10 Bulus ya bayyana dalilin da ya sa ya kamata mu so juna sa’ad da ya ce: “Ku yafa zuciya ta tausayi, nasiha, tawali’u, ladabi, jimrewa; kuna haƙuri da juna, kuna gafarta ma juna, idan kowane mutum yana da maganar ƙara game da wani; kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku, hakanan kuma sai ku yi: gaba da dukan waɗannan kuma ku yafa ƙauna, gama ita ce magamin kamalta.” (Kol. 3:12-14) Ko da a ina ne muka girma, ko da daga wace ƙasa muka fito, ƙauna tana sa mu kasance da haɗin kai da babu irinsa. Hakika, hakan abin godiya ne.
11. Mene ne ƙauna da haɗin suka nuna game da Shaidun Jehobah?
11 Da yake bayin Jehobah suna nuna ƙauna ta gaskiya da kuma haɗin kai, hakan ya nuna cewa su ne suke bin addini na gaskiya. Yesu ya ce: “Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.” (Yoh. 13:34, 35) Ƙari ga haka, manzo Yohanna ya rubuta cewa: “Inda ’ya’yan Allah sun bayyanu ke nan, da ’ya’yan Shaiɗan: dukan wanda ba shi aika adalci ba, ba na Allah ba ne, da wannan kuma wanda ba ya yi ƙaunar ɗan’uwansa ba. Gama jawabi ke nan da kuka ji tun daga farko, mu yi ƙaunar junanmu.” (1 Yoh. 3:10, 11) Ƙauna da haɗin kai sun nuna cewa Shaidun Jehobah ne mabiyan Yesu na gaskiya kuma Allah yana amfani da su wajen yin wa’azin bishara ta Mulki a faɗin duniya.—Mat. 24:14.
JEHOBAH YANA TARA “TARO MAI GIRMA”
12, 13. Mene ne waɗanda suke cikin “taro mai girma” suke yi yanzu, kuma mene ne za su shaida nan ba da daɗewa ba?
12 Yawancin bayin Jehobah a yau suna cikin “taro mai girma” da suka fito daga dukan al’ummai da kabilai da jama’a da kuma harsuna. Su wane ne “taro mai girma”? “Su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala, sun wanke rigunansu, suka mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan,” don suna ba da gaskiya ga fansar da Yesu ya yi. Waɗanda suke cikin “taro mai girma” suna ƙaunar Jehobah da kuma Ɗansa kuma ‘suna bauta ma [Allah] dare da rana.’—R. Yoh. 7:9, 14, 15.
13 Nan ba da daɗewa ba, Allah zai halaka wannan mugun zamani a lokacin “ƙunci mai-girma.” (Mat. 24:21; karanta Irmiya 25:32, 33.) Amma zai ceci bayinsa kuma ya shigar da su cikin sabuwar duniya don yana ƙaunarsu. Shekaru 2,000 da suka shige, Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa Allah “zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.” Shin kana marmarin ganin lokacin da al’amura na dā za su shuɗe? —R. Yoh. 21:4.
14. Ka bayyana yadda waɗanda suke cikin taro mai girma suke ƙaruwa.
14 Bayin Jehobah wajen dubu biyar ne kawai a faɗin duniya a lokacin da aka soma kwanaki na ƙarshe a shekara ta 1914. Da taimakon ruhu mai tsarki, waɗannan bayin Jehobah shafaffu Kiristoci sun yi wa’azin bishara ta Mulki da ƙwazo don suna ƙaunar maƙwabtansu. Mene ne sakamakon? An soma tattara waɗanda suke cikin taro mai girma. Yanzu, Shaidun Jehobah wajen miliyan takwas ne suke tarayya da ikilisiyoyi fiye da 115,400 a faɗin duniya kuma muna ci gaba da ƙaruwa. Alal misali, mutane fiye da 275,500 ne suka yi baftisma a shekarar hidima ta 2014, wato kimanin mutane 5,300 a kowane mako.
15. Ka kwatanta yadda ake samun ci gaba a wa’azin bishara da muke yi.
15 Abin ban al’ajabi ne ganin yadda mutane a faɗin duniya suke sauraron wa’azin bishara ta Mulki. A yau ana buga littattafanmu a harsuna fiye da 700. Mujallar da aka fi rarrabawa a faɗin duniya ita ce Hasumiyar Tsaro. A kowane wata, ana buga fiye da kofi 52,000,000 kuma ana wallafa mujallar a cikin harsuna 247. Ƙari ga haka, an buga littafin nan da muke yin nazari da shi, wato Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? fiye da 200,000,000 a harsuna sama da 250.
16. Mene ne ya sa ƙungiyar Jehobah take samun ci gaba?
16 Ƙungiyar Jehobah tana samun ci gaba a yau don mun ba da gaskiya ga Allah kuma mun amince da Kalmarsa da aka rubuta bisa ja-gorar ruhu mai tsarki. (1 Tas. 2:13) Wani abin da yake da ban mamaki shi ne yadda Jehobah yake yi mana albarka duk da ƙiyayya da tsanantawa da muke fuskanta daga Shaiɗan,“allah na wannan zamani.”—2 Kor. 4:4.
KA ƘAUNACI MUTANE A KOYAUSHE
17, 18. Yaya ya kamata bayin Allah su bi da waɗanda ba Shaidun Jehobah ba?
17 Yaya ya kamata bayin Jehobah su bi da waɗanda ba Shaidun Jehobah ba? Sa’ad da muke wa’azi, muna haɗuwa da mutane dabam-dabam. Wasu suna sauraronmu, wasu kuma suna tsananta mana. Ko da mutane sun saurari wa’azinmu ko ba su saurara ba, Littafi Mai Tsarki ya bayyana yadda ya kamata bayin Jehobah su bi da kowane mutum. Ya ce: “Bari zancenku kullum ya kasance tare da alheri, gyartace da gishiri, domin ku sani yadda za ku amsa tambayar kowa.” (Kol. 4:6) Sa’ad da muke bayyana imaninmu ga mutane, ya kamata mu yin hakan “da tawali’u da bangirma” don muna ƙaunar maƙwabtanmu.—1 Bit. 3:15, LMT.
18 Ko da mutane sun ƙi su saurare mu kuma suka gaya mana baƙar magana, mu nuna cewa muna ƙaunar maƙwabtanmu ta bin misalin Yesu. “Sa’anda aka zage shi, ba ya mayar da zagi ba; sa’anda ya sha azaba, ba ya yi kashedi ba; amma ya danƙa maganatasa ga [Jehobah] wanda ke yin shari’a mai-adalci.” (1 Bit. 2:23) Saboda haka, bai kamata bayin Jehobah su mayar da ‘zagi da zagi ba; amma akasin wannan suna rama da albarka.’—1 Bit. 3:8, 9.
19. Wace ƙa’ida ce Yesu ya ba da game da yadda za mu bi da waɗanda suke gāba da mu?
19 Kasancewa da tawali’u yana taimaka wa bayin Jehobah su bi wata ƙa’ida mai muhimmanci da Yesu ya bayar. Sa’ad da yake ba da huɗuba a kan dutse, ya ce: “Kun dai ji an faɗa, ‘Ka so ɗan’uwanka, ka ƙi magabcinka.’ Amma ni ina gaya muku, ku ƙaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu’a, domin ku zama ’ya’yan Ubanku wanda ke cikin Sama. Domin yakan sa rana . . . ta fito kan mugaye da kuma nagargaru, ya kuma sako ruwan sama ga masu adalci da marasa adalci.” (Mat. 5:43-45) Hakika, a matsayinmu na bayin Allah, wajibi ne mu ‘mu ƙaunaci magabtanmu’ ko da mene ne suka yi mana.
20. Me ya sa dukan mutane za su ƙaunaci Allah da maƙwabtansu a sabuwar duniya? (Ka duba hoton da ke shafi na 21.)
20 Wajibi ne mu nuna cewa muna ƙaunar Jehobah da kuma maƙwabtanmu a duk abubuwan da muke yi. Alal misali, ya kamata mu taimaki waɗanda suke cikin mawuyacin yanayi ko da sun ƙi sauraron wa’azin bishara ko kuma suna tsananta mana. Manzo Bulus ya ce: “Kada . . . ku riƙe bashin kome ga kowa, sai dai na ƙaunar juna: gama wanda ya ƙaunace maƙwabcinsa ya cika shari’a. Gama wannan, Ba za ka yi zina ba, Ba za ka yi kisankai ba, Ba za ka yi sata ba, Ba za ka yi ƙyashi ba, kuma idan da wata doka, an tarke ta cikin wannan magana, cewa, sai ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka. Ƙauna ba ta aika mugunta ga maƙwabcinta ba; ƙauna fa cikar shari’a ce.” (Rom. 13:8-10) A matsayinmu na Shaidun Jehobah, muna nuna ƙauna ta gaske a wannan duniyar Shaiɗan da rashin jituwa da mugunta suka zama ruwan dare. (1 Yoh. 5:19) Babu shakka, ƙauna za ta mamaye duniya bayan Jehobah ya halaka wannan mugun zamani, da Shaiɗan da kuma aljanunsa. Za mu ji daɗin rayuwa a wannan lokacin da dukan waɗanda suke raye a duniya za su ƙaunaci Allah da kuma maƙwabtansu!