Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Abubuwan da Mulkin Allah Ya Cim ma a Cikin Shekara Dari

Abubuwan da Mulkin Allah Ya Cim ma a Cikin Shekara Dari

“Allah na salama . . . ya kamilta ku cikin kowane kyakkyawan abu garin ku aika nufinsa.”—IBRAN. 13:20, 21.

WAƘOƘI: 136, 14

1. Ta yaya Mulkin Allah yake da muhimmanci a wajen Yesu? Ka bayyana.

YESU yana so yin magana game da Mulkin Allah. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ya yi magana game da Mulkin Allah fiye da komai a lokacin da yake duniya. Ya ambaci Mulkin fiye da sau 100 sa’ad da yake wa’azi. Hakika, Mulkin Allah yana da muhimmancin a gare shi.—Karanta Matta 12:34.

2. Mutane nawa ne suka saurari umurnin Yesu a cikin Matta 28:19, 20, kuma me ya sa muka ce haka? (Ka duba ƙarin bayani.)

2 Jim kaɗan bayan Yesu ya tashi daga matattu, ya haɗu da almajirai fiye da 500. (1 Kor. 15:6) Wataƙila a lokacin ne ya ba da umurni cewa su yi wa’azin bishara ga “dukan al’ummai.” * Ƙari ga haka, Yesu ya gaya wa almajiransa cewa wannan babban aiki ne kuma suna bukatar su yi aikin “har matuƙar zamani.” Hakika, mu ma muna cikin waɗanda suke taimaka wa don cika wannan umurni da kuma annabci.—Mat. 28:19, 20.

3. Waɗanne hanyoyi uku ne suka taimaka mana a yin wa’azin bishara?

3 Bayan Yesu ya ba da umurni cewa a yi wa’azi, ya yi wa mabiyansa alkawari cewa: “Ina tare da ku.” (Mat. 28:20) Hakan ya nuna cewa Yesu zai ja-goranci wannan aikin. Kuma Allahnmu ya ba mu “kowane kyakkyawan abu” don mu iya cika wannan umurni. (Ibran. 13:20, 21) A wannan talifin, za mu tattauna wasu kyawawan abubuwa guda uku: (1) kayayyakin aiki da muke amfani da su don wa’azi, (2) hanyoyin da muka yi amfani da su da kuma (3) horarwa da muka samu don yin wa’azi. Bari mu fara da tattauna kayayyakin aikin da muka yi amfani da su a shekaru 100 da suka shige.

SARKIN YA SHIRYA BAYINSA DON SU YI WA’AZI

4. Me ya sa muke yin amfani da kayayyakin aiki dabam-dabam?

4 Yesu ya kwatanta “zancen mulkin” da irin da aka shuka a wurare dabam-dabam. (Mat. 13:18, 19) Manomi zai yi amfani da kayayyakin aiki dabam-dabam don ya shirya gonarsa kafin ya soma shuki. Hakazalika, a waɗannan shekaru da suka shige, Sarkin ya ba mu kayayyakin aiki da za mu yi amfani da su don mu taimaka wa miliyoyin mutane su amince da wa’azin bishara ta Mulki. An yi amfani da waɗansu a ɗa, wasu kuma ana kan amfani da su har yanzu. Amma dukan waɗannan kayayyakin aiki sun taimaka mana mu ƙware a yin wa’azi.

5. Mene ne testimony card, kuma yaya ake amfani da shi?

5 A shekara ta 1933, an soma amfani da wani kayan aiki da ake kira testimony card kuma ya taimaka wa ’yan’uwa da yawa. Wannan wani ƙaramin katin wa’azi ne da ke ɗauke da gajeren saƙon Littafi Mai Tsarki. A wani lokaci ana buga sabon kati kuma a canja saƙon da ke ciki. Yadda ake gudanar da shi ba shi da wuya! Wani ɗan’uwa mai suna C.  W. Erlenmeyer yana ɗan shekara goma da ya soma yin wa’azi da wannan kayan aiki. Ya ce: “Za mu ba wa magidanci katin wa’azi kuma mu ce, ‘Don Allah ka karanta wannan katin.’ Bayan da ya gama karantawa sai mu ba shi littafi kuma mu yi tafiyar mu.”

6. Ta yaya katin wa’azi ya taimaka wa masu shela?

6 Wannan katin ya taimaka wa masu shela a hanyoyi dabam-dabam. Alal misali, wasu masu shela suna jin kunya. Ba su san abin da za su faɗa ba duk da cewa suna son su yi wa mutane wa’azi. Wasu kuma suna da abin faɗa da yawa. Za su iya gaya wa magidanci kome da suka sani a cikin ’yan mintoci, amma ba sa yin hakan yadda ya kamata! Akasin haka, katin wa’azi ya taimaka wa masu shela su yi wa’azi a sauƙaƙe.

7. Waɗanne ƙalubale ne wasu suka fuskanta sa’ad da suke amfani da katin a wa’azi?

7 Hakika, ’yan’uwanmu sun fuskanci ƙalubale a yin amfani da wannan katin. Wata ’yar’uwa mai suna Grace A. Estep da ta daɗe da zama Mashaidiyar Jehobah, ta ce: “A wani lokaci mutane sukan tambaye mu ‘Mene ne katin yake magana a kai?’ Ba za ka iya gaya min ba?’” Wasu magidanta ba su iya karatu ba. Wasu kuma suna gani kamar an ba su katin kyauta ne. Saboda haka, sai su karɓi katin kuma su rufe ƙofarsu. Idan magidanci ba ya so saƙonmu, sai ya yayyage katin. Duk da haka, wannan katin ya taimaka wa masu shela su yi wa’azi ga mutane kuma hakan ya sun san mu a matsayin masu wa’azi bishara ta Mulki.

8. Ka bayyana yadda aka yi amfani da garmaho a wa’azi. (Ka duba hoton da ke shafi na 26.)

8 Wani kayan aiki da aka yi amfani da shi bayan shekara ta 1930 shi ne garmaho. Wasu suna kiran wannan kayan aiki da suna Haruna domin garmahon ne yake yi musu yawancin wa’azi. (Karanta Fitowa 4:14-16.) Idan magidanci ya yarda, sai mai shela ya kunna wani ɗan gajere jawabin wa magidanci ya saurara. Bayan haka, sai mai shelan ya ba shi littattafai. A wani lokaci, iyalai sukan taru don su saurari jawabi daga Littafi Mai Tsarki. A shekara ta 1934, ƙungiyar Jehobah ta soma samar da garmaho musamman don a yi amfani da su a wa’azi. A sannu a hankali, an tanadar da sautin jawabai guda 92.

9. Ta yaya garmaho ya taimaka a wa’azi?

9 Sa’ad da wani magidanci mai suna Hillary Goslin ya ji waɗannan jawaban Littafi Mai Tsarki, sai ya karɓi garmaho daga wurin wani mai shela na sati ɗaya don ya yi amfani da shi wajen yi wa maƙwabtansa wa’azi. Lokacin da mai shelan ya dawo, sai ya ga cewa mutane suna jiran sa don sun ji daɗin wa’azin. Da shigewar lokaci, waɗannan mutane sun yi baftisma. Daga baya, ’ya’yan Hillary mata biyu, sun halarci Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead kuma suka zama masu wa’azi a ƙasar waje. Kamar katin wa’azi, garmaho ya taimaka wa mutane su soma yin wa’azi. Daga baya, Sarkin ya yi amfani da Makarantar Hidima ta Allah don ya koyar da mutanensa yadda za su yi wa’azi.

YIN AMFANI DA HANYOYI DABAM-DABAM WAJEN YIN WA’AZI

10, 11. Ta yaya aka yi amfani da jarida da kuma rediyo wajen yaɗa bishara ta Mulki, kuma me ya sa waɗannan hanyoyin suke da sauƙi da kuma inganci?

10 Sarkin yana ja-gorar mutanen Allah su yi amfani da hanyoyi dabam-dabam don yi wa mutane wa’azi. Hakan yana da muhimmanci a lokacin domin ‘ma’aikatan kaɗan ne.’ (Karanta Matta 9:37.) Alal misali, a lokacin an yi amfani da jarida don wannan wa’azin bishara ya kai wuraren da Shaidun Jehobah ba su da yawa. Kowane mako, ɗan’uwa Charles Taze Russell yana aika jawaban Littafi Mai Tsarki ga wata ƙungiyar da ke samar da labarai. Bayan haka, sai wannan ƙungiyar ta aika jawaban ga kafofin yaɗa labarai a ƙasashen Kanada da Amirka da kuma a ƙasashen Turai. A shekara ta 1913, jaridu da ke yaɗa jawaban Ɗan’uwa Russell sun kai 2,000 kuma kimanin mutane miliyan 15 ne suke karanta jawaban!

11 An fitar da wata sabuwar hanyar yaɗa wa’azin bishara bayan da Ɗan’uwa Russell ya rasu. A ranar 16 ga Afrilu, a shekara ta 1922, Ɗan’uwa Joseph F. Rutherford ya ba da ɗaya daga cikin jawabansa na farko a tashar rediyo kuma kimanin mutane 50,000 ne suka saurari jawabin. A ranar 24 ga Fabrairu, a shekara ta 1924 ne aka soma yaɗa labarai a tashar rediyonmu da ake kira WBBR. Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 1924 ta yi bayani game da wannan hanyar yaɗa bishara ta rediyo. Ta ce: “Hakika, rediyo shi ne hanya mafi sauƙi da kuma inganci na yaɗa wa’azin bishara ta Mulki.” Kamar jarida, rediyo ya taimaka wajen yaɗa bishara ta Mulki ga mutane a wuraren da Shaidun Jehobah ba su da yawa.

Masu shela da yawa suna jin daɗin yin wa’azi ga jama’a kuma suna nuna wa mutane dandalinmu na jw.org (Ka duba sakin layi na 12, 13)

12. (a) Wane tsarin wa’azi ga jama’a ne ka fi so? (b) Mene ne zai taimaka mana mu sha kan tsoro sa’ad da muke wa’azi a wuraren da jama’a suke?

12 Wa’azi a inda akwai jama’a wata hanya ce da ake amfani da ita wajen sanar da mutane game da Mulkin Allah. Hakan ya ƙunshi yin wa’azi a tashoshin bas da tashoshin jirgin ƙasa da wuraren ajiye motoci da kasuwa da kuma wasu wurare da jama’a suke taruwa. Shin kana jin tsoron yin wa’azi a wannan hanyar? Idan hakan ne, ka yi addu’a ga Jehobah don ya taimake ka. Ka yi la’akari da abin da wani Ɗan’uwa mai suna Manera Angelo Jr., da ya daɗe yana hidimar mai kula mai ziyara ya ce: “Idan aka fitar da wata sabuwar hanyar wa’azi, muna ɗaukawa a matsayin damar bauta wa Jehobah a wata hanya da kuma kasancewa da aminci a gare shi. Ƙari ga haka, muna a shirye mu nuna masa cewa za mu bauta masa da yardar rai a kowace hanyar da yake so.” Idan muka sha kan kunya da kuma tsoro, za mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah kuma mu ƙware a yin wa’azi.—Karanta 2 Korintiyawa 12:9, 10.

13. Me ya sa yin amfani da dandalinmu na jw.org a wa’azi yake da amfani, kuma ta yaya ka yi amfani da shi wajen taimaka wa mutane?

13 Masu shela da yawa suna ji daɗin gaya wa mutane game da dandalinmu na jw.org, domin su karanta da kuma sauko da littattafanmu a harsuna fiye da 700. Mutane fiye da miliyan ɗaya da dubu ɗari shida ne suke shigan dandalinmu a kowace rana. A yau, ana yaɗa bishara ta Mulki ga mutane a faɗin duniya ta dandalinmu kamar yadda aka yi ta rediyo a dā.

YADDA AKE KOYAR DA MASU HIDIMA DON SU YI WA’AZI

14. Wace horarwa ce masu shela suke bukata, kuma wace makarantar ce ta taimaka musu su ƙware a yin wa’azi?

14 Mun tattauna wasu kayayyakin aiki da kuma hanyoyin yaɗa bishara ta Mulki. Amma masu shela suna bukatar horarwa don su zama masu hidima da suka ƙware. Alal misali, a wani lokaci, magidanta ba sa yarda da abin da suka ji a garmaho. A wani lokaci kuma, sukan ji daɗin abin da suka karanta kuma su so ƙarin bayani. Saboda haka, masu shela suna bukatar su san yadda za su bi da waɗanda ba sa so saƙonmu da kuma taimaka wa waɗanda suka so saƙonmu. Ta wurin ja-gorar ruhu mai tsarki, Nathan H. Knorr ya ga cewa ya dace a horar da masu shela don su san yadda za su yi wa mutane magana sa’ad da suka fita wa’azi. Mene ne sakamakon? A shekara ta 1943, an ƙaddamar da Makarantar Hidima ta Allah a ikilisiyoyi kuma wannan makarantar ta taimaka mana mu ƙware a yin wa’azi.

15. (a) Yaya waɗansu suka ji sa’ad da suke ba da jawabi a Makarantar Hidima ta Allah? (b) Ta yaya Jehobah ya taimaka maka kamar yadda ya yi alkawari a littafin Zabura 32:8?

15 ’Yan’uwa da yawa ba su saba yin magana a gaban mutane ba. Wani Ɗan’uwa mai suna Julio S. Ramu ya tuna da jawabinsa na farko a makarantar a shekara ta 1944. Jawabin a kan wani mutum ne da aka ambata a Littafi Mai Tsarki mai suna Doeg! Ya ce: “Gwiwowina da hannayena da kuma haƙorana duk rawa suke yi.” Ya ƙara cewa: “Na ba da jawabin a cikin minti uku kuma wannan shi ne lokaci na farko da na ba da jawabi ga mutane, amma ban karaya ba.” Yara ma suna ba da jawabi a makarantar ko da shi ke ba shi da sauƙi wa wasu su ba da jawabi a gaban ’yan’uwa a ikilisiya. Ɗan’uwa Angelo Manera da aka ambata ɗazu, ya tuna da wani yaro da ya ba da jawabinsa na farko kuma ya ce: “Ya tsorata sa’ad da ya fara ba da jawabin har ya soma kuka. Amma ya nace, saboda haka, sai ya ci gaba da ba jawabin yana kuka, har ya gama ba da jawabin.” Shin kana jinkirin ba da kalami ko kuma saka hannu a wasu shirye-shiryen taro saboda tsoro ko kunya? Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka sha kan tsoro. Zai taimaka maka kamar yadda ya taimaka wa waɗannan ɗaliban farko na Makarantar Hidima ta Allah.—Karanta Zabura 32:8.

16. Mene ne Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead ta cim ma (a) a dā da kuma (b) tun shekara ta 2011?

16 Ƙungiyar Jehobah ta sake samar da wata hanyar horar da masu shela ta Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gilead. Masu wa’azi a ƙasashen waje da kuma wasu masu shela sun amfana sosai ta wajen halartar wannan makarantar. Wani malamin makarantar ya ce makarantar yana “ƙarfafa ɗaliban su kasance da sha’awar yin wa’azin bishara.” An ƙaddamar da wannan makarantar a shekara ta 1943. Kuma tun lokacin, an horar da mutane fiye da 8,500. Masu wa’azi a ƙasashen waje da suka sauke karantu daga makarantar sun yi hidima a wajen ƙasashe 170. Tun daga shekara ta 2011, waɗanda suke hidima ta cikkaken lokaci ne kawai ake gayyata zuwa makarantar, wato majagaba na musamman da masu kula masu ziyara da masu hidima a Bethel da kuma masu wa’azi a ƙasashen waje da ba su je Gilead ba.

17. Ta yaya horarwar da ake yi a makarantar Gilead ta kasance da amfani?

17 Shin wannan horarwar ta kasance da amfani kuwa? Ka yi la’akari da wannan misalin. A watan Agusta na shekara ta 1949, masu shela a ƙasar Japan ba su kai goma ba. Amma a ƙarshen wannan shekara, masu wa’azi a ƙasar waje da suka sauke karatu a makarantar Gilead guda 13 suna hidima da ƙwazo a ƙasar. A yau, masu shela a ƙasar Japan sun kai 216,000, kuma kusan kashi 42 ne suke hidima a matsayin majagaba!

18. Ka ambaci sunayen wasu makarantu da suka taimaka wa Shaidun Jehobah su ƙarfafa bangaskiyarsu.

18 Waɗansu makarantu kamar Makarantar Hidima ta Mulki da Makarantar Hidima ta Majagaba da Makarantar Koyar da Masu Hidima da Makaranta Don Masu Kula Masu Ziyara da Matansu, da kuma Makaranta Don Mambobin Kwamitin da Ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah da Matansu, sun taimaka wajen horar da ’yan’uwa su ƙarfafa bangaskiyarsu. Babu shaka, Sarkin ya ci gaba da horar da bayinsa.

19. Mene ne Charles Taze Russell ya ce game da wa’azin bishara, kuma yaya hakan ya zama gaskiya?

19 Sama da shekaru 100 sun shige da Mulkin Allah ta soma sarauta. Sarkinmu Yesu Kristi ya ci gaba da horar da mu. Charles Taze Russell ya nuna cewa za a yi wannan wa’azin bishara ta Mulki a duk faɗin duniya kuma kafin mutuwarsa a shekara ta 1916, ya ce: “Wannan aiki yana ci gaba kuma zai ci gaba da ƙaruwa, gama za a yi wa’azin bishara ta Mulki sosai a ‘dukan faɗin duniya.’” (Faith on the March, A. H. Macmillan, shafi na 69) Hakan gaskiya ne. Muna godiya cewa Allah na salama ya ci gaba da tanadar mana da abubuwan da muke bukata don mu yi wannan aiki mafi muhimmanci! Hakika, yana ba mu “kowane kyakkyawan abu” don mun cim ma nufinsa!

^ sakin layi na 2 Muna da tabbacin da ya nuna cewa yawancin waɗanda suke wajen a lokacin sun zama Kiristoci. A wasiƙar manzo Bulus zuwa ga Korintiyawa, ya ce waɗannan ‘’yan’uwa, sun yi ɗari biyar.’ Ya ƙara cewa: “A cikinsu fa yawanci sun wanzu har wa yau, amma waɗansu sun rigaya sun yi barci.” Hakan ya nuna cewa manzo Bulus da sauran Kiristoci sun san ’yan’uwa da yawa da suka saurari umurnin Yesu.