ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ƘARSHEN DUNIYA YA KUSA KUWA?
Mene ne Ra’ayinka Game da “Karshen” Duniya?
Mene ne kake tunani a kai sa’ad da ka ji furucin nan “Ƙarshe ya kusa!” Kana tunanin zuwan Almasihu ne don ya kai mutane masu adalci zuwa sama sa’an nan ya halaka miyagu ko kuwa kana tunanin cewa wani ya mutu ne? Irin wannan yanayin yana iya tsoratar da wasu ko kuma ya sa su alhini.
Littafi Ma i Tsarki ya ce: ‘Ƙarshen zai zo.’ (Matta 24: 14, Littafi Mai Tsarki) Ana kuma kiran wannan ƙarshen “babbar rana ta Allah” da kuma “Armagedon.” (Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16) Babu shakka, addinai da yawa sun ruɗe a kan wannan batun kuma akwai ra’ayoyi dabam-dabam game da ƙarshen duniya. Amma, Littafi Mai Tsarki ya faɗi dalla-dalla abin da ƙarshen yake nufi da kuma abin da ba ya nufi. Kalmar Allah ta kuma taimaka mana mu san ko ƙarshen ya kusa. Bugu da ƙari, ta koya mana yadda za mu iya tsira a wannan ranar! Bari mu fara yin bayani a kan mummunar fahimtar da wasu suke da shi game da ƙarshen, sa’an nan mu bayyana abin da ƙarshen yake nufi. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da ƙarshen duniya?
ABIN DA ƘARSHEN BA YA NUFI
-
ƘARSHEN BA YA NUFIN HALAKA DUNIYA GABA ƊAYA DA WUTA.
Littafi Mai Tsarki ya ce: “[Allah] ya kafa tussan duniya, domin kada ta jijjigu har abada.” (Zabura 104:5) Wannan ayar da kuma wasu ayoyi cikin Littafi Mai Tsarki sun tabbatar mana cewa Allah ba zai halaka doron ƙasa ba kuma ba zai taɓa ƙyale a halaka ta ba!—Mai-Wa’azi 1:4; Ishaya 45:18.
-
ƘARSHEN BA YA NUFIN HALAKA DUNIYA BA ZATO BA SAMMANI.
Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah ya riga ya ƙayyade lokacin da ƙarshe zai zo. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zancen ranan nan da sa’an nan ba wanda ya sani, ko mala’iku cikin sama, ko Ɗan, sai Uban. Ku yi lura, ku yi tsaro, ku yi addu’a: gama ba ku san lokacin da sa’a take ba.” (Markus 13:32, 33) Babu shakka, Allah wanda shi ne “Uban” ya riga ya ƙayyade ‘sa’ar’ da ƙarshen zai zo.
-
BA ’YAN ADAM KO WASU ABUBUWA DA KE FAƊOWA DAGA SARARIN SAMA NE ZA SU KAWO ƘARSHEN BA.
Me zai sa ƙarshen ya zo? Littafin Ru’ya ta Yohanna 19:11 ta ce: “Sai na ga sama a buɗe; ga kuma wani farin doki, da mahayinsa, ana ce da shi Mai-aminci da Mai-gaskiya.” Aya 19 ta ce: “Na ga dabbar kuma, da sarakuna na duniya, da rundunar yaƙinsu, a tattare domin su yi yaƙi da wanda yake zaune bisa dokin, da rundunarsa kuma.” (Ru’ya ta Yohanna 19:11-21) Ko da yake yawancin abubuwa da aka ambata a nan ba a zahiri ba ne, amma a bayyane yake cewa Allah zai aiko da mala’ikunsa su halaka maƙiyansa.
ABIN DA ƘARSHEN YAKE NUFI
-
ƘARSHEN GWAMNATIN ’YAN ADAM.
Littafi Mai Tsarki ya yi bayani cewa: “Allah mai-sama za ya kafa wani mulki, wanda ba za a rushe shi ba daɗai, sarautarsa kuwa ba za a bar wa wata Daniyel 2:44) Kamar yadda aka nuna a baya a sakin layi na 3, za a halaka “sarakuna na duniya, da rundunar yaƙinsu” waɗanda za su taru “domin su yi yaƙi da wanda yake zaune bisa dokin, da rundunarsa kuma.”—Ru’ya ta Yohanna 19:19.
al’umma ba; amma za ya farfashe dukan waɗannan mulkoki ya cinye su, shi kuwa za ya tsaya har abada.” ( -
ƘARSHEN YAKE-YAKE DA MUGUNTA DA KUMA RASHIN ADALCI.
“[Allah] ya sa yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya.” (Zabura 46:9) “Masu-adalci za su zauna cikin ƙasan, kamilai kuma za su wanzu a cikinta. Amma za a datse miyagu daga cikin ƙasan, za a tumɓuke masu-cin amana kuma.” (Misalai 2:21, 22) Allah ya ce: “Duba, sabonta dukan abu nake yi.”—Ru’ya ta Yohanna 21:4, 5.
-
ƘARSHEN ADDINAN DA SUKA ƘI YIN NUFIN ALLAH KUMA SUKA CUTAR DA ’YAN ADAM.
Littafi Mai Tsarki ya ce: “Annabawa sun yi annabcin ƙarya, firistoci kuma sun yi mulki da ikon kansu, . . . Amma sa’ad da ƙarshe ya zo, me za ku yi?” (Irmiya 5:31, LMT) Yesu kuma ya ce: “A cikin wannan rana mutane da yawa za su ce mani, Ubangiji, Ubangiji, ba mu yi annabci da sunanka ba, da sunanka kuma muka fitar da aljanu, da sunanka kuma muka yi ayyuka da yawa masu-iko? Sa’an nan zan furta masu, ban taɓa saninku ba daɗai: rabu da ni, ku masu-aikata mugunta.”—Matta 7:21-23.
-
ƘARSHEN MUTANEN DA KE JAWO MATSALOLI A YAU.
Yesu Kristi ya ce: “Shari’a fa ke nan, haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka fi son duhu da haske; domin ayyukansu miyagu ne.” (Yohanna 3:19) Littafi Mai Tsarki ya yi bayani a kan lokacin da aka halaka miyagu a zamanin Nuhu wanda shi mutumi ne mai adalci. ‘Duniyar wancan zamani, ruwa ya sha kanta, ta halaka. Ta maganar Allah ne kuma sama da ƙasa da ke nan yanzu, aka tanada su ga wuta, ana ajiye su, har zuwa ranan nan da za a yi wa marasa bin Allah shari’a, a halaka su.’—2 Bitrus 3:5-7, LMT.
Ka lura cewa an gwada “ranan nan da za a yi wa marasa bin Allah shari’a” da halaka ‘duniya’ da aka yi a zamanin Nuhu. Wace duniya ce aka halaka? Babu shakka, ba a halaka doron ƙasa ba, amma mutane “marasa bin Allah,” wato maƙiyan Allah ne aka “halaka.” A wannan ranar “shari’a” da ke tafe, Allah zai halaka dukan mutanen da suke yin gāba da shi. Amma dukan aminan Allah za su sami ceto kamar yadda aka cetar da Nuhu da iyalinsa.—Matta 24:37-42.
Ka yi tunanin irin jin daɗin da za a riƙa yi a wannan duniyar sa’ad da Allah ya cire dukan miyagun mutane da tasirinsu! Babu shakka, abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da ƙarshe ba abin fargaba ba ne amma albishiri ne. Duk da haka, kana iya cewa: ‘Shin Littafi Mai Tsarki ya faɗi ranar da ƙarshen zai zo? Ƙarshen ya kusa kuwa? Me ya kamata in yi don in tsira a wannan ranar?’