Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Za mu iya sanin gaskiya game da Allah kuwa?
Allah ya taɓa magana da mutane a dā. Ya yi amfani da ruhunsa mai tsarki ko ikonsa don ya taimaka wa mutane su rubuta abin da yake so. (2 Bitrus 1:20, 21) Za mu iya sanin gaskiya game da Allah ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki.—Karanta Yohanna 17:17; 2 Timotawus 3:16.
Allah ya bayyana abubuwa da yawa game da kansa a cikin Littafi Mai Tsarki. Ya faɗi dalilin da ya sa ya halicci mutane da nufinsa gare su da kuma yadda za su yi rayuwa. (Ayyukan Manzanni 17:24-27) Jehobah Allah yana so mu san gaskiya game da shi.—Karanta 1 Timotawus 2:3, 4.
Me ya sa Allah yake ƙaunar masu son gaskiya?
Jehobah, Allah ne na gaskiya kuma ya aiko da Ɗansa zuwa duniya don ya koya wa mutane gaskiya. Saboda haka, mutane masu son gaskiya suna ƙaunar Yesu. (Yohanna 18:37) Jehobah yana son irin waɗannan mutanen su zama bayinsa.—Karanta Yohanna 4:23, 24.
Shaiɗan Iblis ya hana mutane da yawa sanin Allah ta wajen yaɗa koyarwar ƙarya game da Allah. (2 Korintiyawa 4:3, 4) Mutanen da ba sa son gaskiya ne suke amincewa da wannan koyarwar ƙarya. (Romawa 1:25) Amma miliyoyin mutane suna neman gaskiya game da Allah ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki.—Karanta Ayyukan Manzanni 17:11.