Cutar Karancin Jini da Maganinsa
Wata me suna Beth ta ce, “Na kamu da cutar karancin jini (Anemia) sa’ad da nake matashiya. A lokacin, jikina yana yawan mutuwa kuma ina saurin gajiya, duk kasusuwana sun ta min ciwo kuma yakan yi min wuya in tattara hankali waje daya. Likitana ya ba ni magungunan da suke kunshe da sinadarin iron. Cin abinci mai kyau da kuma magungunan ne suka sa na soma samun sauki.”
Mutane da yawa suna fama da irin rashin lafiyar da Beth ta yi fama da shi. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce, mutane biliyan biyu, wato wajen mutane 30 cikin 100 a duk duniya, suna fama da cutar karancin jini. Kuma a kasashe masu tasowa, mata masu juna biyu wajen 50 cikin 100 ne suke fama da wannan cutar. Ban da haka ma, kashi 40 cikin 100 na yara masu shekara 3 zuwa 5 suna fama da cutar.
Cutar karancin jini tana da hadari sosai. Idan ta yi tsanani, za ta iya kai ga ciwon zuciya. Hukumar Lafiya ta Duniya ta kuma ce, a wasu kasashe, cutar karancin jini ne yake jawo mutuwar kashi 20 cikin 100 na mata masu juna biyu da suke mutuwa. Rashin sinadarin iron ne ya fi jawo cutar karancin jini. Mata masu irin cutar ne suke haihuwa kafin ciki ya kai wata tara, yakan kuma sa su haifi jaririn da ba shi da nauyi. Yara ma da suke fama da wannan cutar ba sa girma da wuri kuma suna saurin kamuwa da cuttutuka. Amma ana iya guje kamauwa da wannan cutar ko kuma a magance ta. a
Me Ake Nufi da Cutar Karancin Jini?
Za a ce mutum yana fama da cutar karancin jini idan ba shi da isashen jajayen kwayoyin jini. Abubuwan da suke jawo cutar nan suna da yawa. Kuma kwararrun masanan kiwon lafiya sun ganu cewa akwai ire-iren cutar karancin jini fiye da 400! Mutum zai iya fama da wannan cutar na dan lokaci ko na dogon lokaci, kuma yana iya zama dama-dama ko da tsanani.
Mene ne Yake Jawo Cutar Karancin Jini?
Ga abubuwa uku da suke sa mutum ya kamu da cutar karancin jini:
Idan mutum ya rasa Jajayen kwayoyin jini na jikinsa.
Idan jikin mutum ya kasa haifar da isashen jajayen kwayoyin jini.
Idan wata cuta a jikin mutum yana hallaka jajayen kwayoyin jini.
Rashin sinadarin iron ne ya fi sa mutane kamuwa da cutar karancin jini. Idan babu isashen iron a jikin mutum, hakan zai iya sa jikin mutum ya kasa haifar da wani sinadarin da ake kira hemoglobin. Kuma sinadarin ne zai iya sa jajayen kwayoyin jini su rika yawo da iskar da muke shaka (oxygen) a jikin mutum.
Alamun Cutar Karancin Jini na Rashin Sinadarin Iron
Da farko, cutar karancin jini ba ta tsanani, wasu ma da suke da cutar ba sa sani cewa suna dauke da ita. Ko da yake alamun suna iya bambanta, ga yawancin alamun da ake gani idan mutum yana da cutar:
Yawan gajiya
Hannayen mutum ko kafafunsa za su rika sanyi
Mutuwar jiki
Fatar mutum na canja kala
Ciwon kai da jiri
Ciwon kirji da yawan faduwar gaba da yankewar numfashi
Farsuna masu kakkaryewa
Rashin son cin abinci, musamman jarirai ko yara
Jin kwadayin shan kankara, da cin sitaci ko kuma datti
Su Waye ne Suke Yawan Kamuwa da Cutar?
Mata ne suka fi kamuwa da cutar domin suna rasa jini sa’ad da suke al’ada. Mata masu juna biyu kuma suna kamuwa da cutar idan ba sa cin abinci da ke da irin sinadarin Bitamin B da ake kira folate ko folic acid.
Jariran da ake haifar su kafin wata tara, ko marasa nauyi domin ba sa samun sinadarin iron daga nonon da suke sha.
Yaran da ba sa ci abinci dabam-dabam masu gina jiki.
Marasa cin nama ko kifi (Vegetarians) da ba sa cin abincin da ke dauke da sinadarin iron.
Masu rashin lafiya mai tsanani, kamar wadanda suke fama da cututtukan jini, ko cutar kansa, ko cutar koda, ko cutar alsa mai tsanani, ko kuma wasu irin cututtuka.
Yadda Za a Magance Cutar Karancin Jini
Ba kowane irin cutar karancin jini ne ake magance shi ba. Amma zai yiwu a guji ko a magance wadda aka samu sanadiyar rashin isashen sinadarin iron. Cin abinci masu gina jiki zai iya taimakawa, kuma ga wasu sinadaran da ya kamata su kasance a abincin da mutum mai dauke da cutar zai rika ci:
Sinadarin Iron. Ana samun iron a nama da wake da lentils da kuma ganyaye kamar su, zogale da karkashi da alaiyaho. b Yin abinci a cikin tukunyan karfe ma yana da kyau don wasu bincike sun nuna cewa yin abinci a tukunyan karfe na sa sinadarin iron ya karu a abincin.
Sinadarin Folate. Ana samun wannan sinadarin a ’ya’yan itace, da ganyaye kamar su zogale da karkashi da alaiyaho, da green peas, da man shanu, da kwai, da kifi, da almon, da kuma gyada. Ana kuma samunsa a burodi, da taliya, da shinkafa, da masara, da dawa da kuma makamantansu. Sinadarin folate da mutane suka sarafa shi ne folic acid.
Sinadarin Bitamin B-12. Ana samun sinadarin nan ne a nama, da madara, da waken soya, da hatsin da aka hada masa sinadarin nan (fortified cereal).
Bitamin C. Ana samunsa a lemu da su jus, da borkonu, da broccoli, da tumatiri, da kankana da kuma strawberry. Abinci mai dauke da bitamin C yana taimaka wa jikinmu ya yi amfani da sinadarin iron.
Akwai abinci iri-iri bisa ga inda kake. Saboda haka, zai dace ka bincika irin abincin da ke da wadannan sinadaran a yankinku. Yin hakan yana da muhimmanci idan ke mace ce mai juna biyu ko kina shirin yin hakan. Idan kin kula da lafiyarki ta wannan hanyar, za ki iya kāre jaririn da za ki haifa daga cutar karancin jini. c
a Bayanan da aka yi a talifin nan game da irin abincin da masu cutar za su rika ci da makamantansu, an samo su ne daga Mayo Clinic da kuma The Gale Encyclopedia of Nursing and Allied Health. Zai fi ka je ka ga likita idan da alamar cewa kana da irin cutar nan.
b Bai kamata ka sha ko ka ba wa danka magunguna masu dauke da sinadarin iron ba tare da umurni daga wurin likita ba. Yawan iron a jikin dan Adam yana illata hantarsa kuma ya jawo wasu cututtuka.
c Wasu likitoci sukan magance cutar ta wajen kara wa mutum jini, amma Shaidun Jehobah ba sa amincewa da hakan.—Ayyukan Manzanni 15:28, 29.