Tone-tone Sun Nuna Inda Wata Kabilar Isra’ila Ta Taba Zama
Baibul ya ce a lokacin da Isra’ilawa suka shiga Kasar Alkawari, kuma aka raba wa kowace kabila kasa, zuriya goma a kabilar Manassa sun sami babban fili a yammacin Urdun, nesa da sauran kabilun. (Yoshuwa 17:1-6) Akwai wani abu da aka tono da ya tabbatar da hakan?
A shekara ta 1910, an tono wasu gutsuren tukwane a Samariya da ke dauke da rubutu. Wadannan gutsurin tukwane na dauke da rubutu a Ibrananci kuma ya nuna kaya masu tsada kamar su ruwan inabi da kuma māi mai tsada da ake kai fādar sarki a birnin. Gutsurori 102 ne aka samo, kuma an yi su ne a karni na takwas kafin haihuwar Yesu, amma guda 63 ne kadai za a iya karantawa. Dukan wadannan gutsurori 63 sun nuna lokaci da sunayen zuriya da sunayen wadanda suke aika da kuma masu karbar kayayyakin.
Hakazalika, duka zuriyar da aka rubuta a gutsurin tukwane a Samariya ʼyan kabilar Manassa ne. Juyin NIV Archaeological Study Bible ya ce hakan ya ba da “karin bayani a kan abin da Baibul ya ce game da zuriyar Manassa da kuma wurin da suka zauna.”
Gutsurarrun tukwane da aka samo a Samariya sun tabbatar da abin da Amos, wani marubucin Baibul ya ce game da masu arziki a lokacin. Ya ce: “Kuna shan ruwan inabi daga manyan kwanoni, kuna shafa wa jikinku māi mafi tsada.” (Amos 6:1, 6) Gutsurarrun tukwanen Samariya sun nuna cewa an shigar da wadannan kayayyakin zuwa inda zuriya goma na Manassa suka mallaka.