Mu Zama Kamar Yara
Ka Saukar:
1. Yesu ya ce mana
Mu zama kamar yara,
A duniyar da babu saukin kai,
Mu zama da halin yara.
Kamar Jehobah, mu rika daraja dukan mutane.
(AMSHI)
Kamar yara, mu kaunaci juna sosai,
Kada mu sa ido ga kuskuren juna.
Kamar yara, mu zama da halin kirki,
Ko yaushe mu ga kokarin ’yan’uwanmu.
2. Sa’ad da muke girma
A duniya mai mugunta,
Za mu iya lura da kuskuren,
Da ’yan’uwanmu suke yi.
Ba a girmama wa mutane a wannan zamanin.
(AMSHI)
Kamar yara, mu kaunaci juna sosai,
Kada mu sa ido ga kuskuren juna.
Kamar yara, mu zama da halin kirki,
Ko yaushe mu ga kokarin ’yan’uwanmu.
Kamar yara fa.
3. Yayin da muke,
Bauta wa Allah,
Da farin ciki
Muna kokari,
Mu tuna cewa
A wannan duniyar,
Mu zama da hali na yara.
(AMSHI)
Kamar yara, mu kaunaci juna sosai,
Kada mu sa ido ga kuskuren juna.
Kamar yara, mu zama da halin kirki,
Ko yaushe mu ga kokarin ’yan’uwanmu.
Kamar yara fa.