Koma ka ga abin da ke ciki

Rumbun Hotuna na Ofishin Filifin na 1 (Fabrairu Zuwa Mayu 2015)

Rumbun Hotuna na Ofishin Filifin na 1 (Fabrairu Zuwa Mayu 2015)

Shaidun Jehobah suna gina sababbin gidaje da kuma gyara wasu gine-gine a ofishinsu da ke Filifin a Quezon City. Tun da a yanzu ofishinmu da ke Japan ne ke buga littattafan da ake amfani da su a Filifin, hakan ya sa aka mai da wurin da ake buga littattafai a dā sashen Kwamfuta da sashen Gine-gine da sashen Gyare-gyare da sashen Sufurin Littattafai da kuma sashen Fassara. A wannan rumbun hotuna, an nuna wasu ayyukan da aka yi daga watan Fabrairu 2014, zuwa Mayu 2015 a wurin da ake buga littattafai a dā da kuma wasu gine-gine. Ana sa rai za a gama wannan aikin a watan Oktoba 2016.

Hoton da ke nuna yadda ofishin Filifin zai kasance sa’ad da aka kammala. Wuraren da ake ginawa da kuma gyarawa su ne:

  • Gini na 4 (Gidan zama)

  • Gini na 5 (Sashen Daukan Sauti da Bidiyo da Sashen Hidima)

  • Gini na 6 (Sassan Tsara Mahalli da Gyara Motoci da kuma Welda)

  • Gini na 7 (Sassan Kwamfuta da Gine-Gine da Gyare-Gyare da Sufurin Littattafai da kuma Fassara)

28 ga Fabrairu, 2014​—Gini na 7

Ma’aikata na dan lokaci suna saka abin rage zafi ko sanyi a gini a cikin buhuna don kada su yi danshi. Suna sanye da wasu tufafi da zai kāre su daga illar da ke tattare da wannan kayan aiki.

2 ga Afrilu, 2014​—Gini na 7

Ma’aikata sun gama silin na sashen daukan sauti da bidiyo don Yaren Kurame a Filifin. Za a saka mafitar iskar iyakwandishan a ramukan da ke silin, hakan zai sa sanyin iyakwandishan ya bazu a ko’ina a dakin daukan sauti da bidiyo.

21 ga October, 2014​—Wurin da Ake Gine-Gine a Quezon City

Ana tona ramin da za a saka bututun ruwan sanyi. Wannan sabon tsarin zai rika kai ruwa a dukan gine-ginen da ke wannan ofishin Shaidun Jehobah.

19 ga Disamba, 2014​—Hanya a gidan sama da za a bi zuwa Gini na 1 da na 5 da kuma na 7

An yi wata sabuwar hanya a jikin gini daga sama da za a iya bi zuwa dukan manyan gine-ginen kuma hakan ya hada da Gini na 1, wato inda gidan abinci yake. Wannan hanyar za ta taimaka wa mutane fiye da 300 da suke aiki a Gini na 7.

15 ga Janairu, 2015​—Gini na 5

Motar daga kaya da za ta iya daga kaya da ya kai nauyin tan hamsin tana daga karafa da za a yi rufin ginin da shi. ’Yan kwangila da ke yankin suna amfani da motocin daga kaya dabam-dabam.

15 ga Janairu, 2015​—Gini na 5A (Mahadan gine-gine)

A wannan mahadan gine-gine mai fadin kafa 1,345, akwai gidajen wanka guda biyu da matakala da kuma lif. Da yake akwai gidan wanka da matakala a ginin, hakan zai sa a sami karin fili kusa da Gini na 5. An saka lif a wannan ginin maimakon a Gini na 5 don kada karar lif ya rika damun ’yan’uwa da ke daukan sauti da bidiyo sa’ad da suke aiki.

15 ga Janairu , 2015​—Gini na 5A (Mahadan gine-gine)

Ma’aikata sun shiga inuwa saboda zafin rana yayin da suke saka karafuna. A watan Janairu, zafin rana yana kai wajen maki 29 a ma’aunin Celsius kuma a watan Afrilu zafin rana yana kai wajen maki 34 a ma’aunin Celsius.

5 ga Maris, 2015​—Gini na 5

Ma’aikata suna amfani da katako don su kara karfin rufin. An yi amfani da katako masu inganci kusan 800 a Gini na 5.

17 ga Maris, 2015​—Gina na 5

Ma’aikata suna kwaba siminti don wani karamin aiki da za su yi. Ma’aikata da suke taimakawa a aikin sun fi 100 daga Ostareliya da Kanada da Faransa da Japan da New Zealand da Koriya ta Kudu da Sifen da Amirka da kuma wasu kasashe.

25 ga Maris, 2015​—Gini na 5

Ma’aikata suna yin rufin karfe mai karfi a Gini na 5 inda Sashen Fassara yake a dā. Ana gyara ginin don zai a mai da shi sashen Daukan Sauti da Bidiyo da kuma Sashen Hidima.

13 ga Mayu, 2015​—Gini na 5

Wata ma’aikaciya tana amfani da zarto don ta yanka karfe da za a yi amfani da shi don inganta bangon ofishin.