Koma ka ga abin da ke ciki

Tana Ci-gaba da Jimre Matsalolinta

Tana Ci-gaba da Jimre Matsalolinta

 Wata Mashaidiyar Jehobah mai suna Virginia tana fama da ciwon da ke hana ta magana da kuma motsa jiki da ake kira Locked-In Syndrome. Jikinta ya shanye. Tana iya gani da kuma ji, ta bude idanunta ko ta rufe su, kuma tana iya motsi da kanta kadan-kadan. Ba ta iya magana ko ta ci abinci. A can baya ita lafiyayyar mace ce mai kuzari. Amma wata rana da safe a 1997 ta ji ciwon kai mai tsanani a keyarta da ya ki sauka. Mijinta ya kai ta asibiti, kuma da yammar ta fita daga hayyacinta. Bayan mako biyu ta dawo hayyacinta kuma ta ga cewa tana daki na musamman da ake kula da masu rashin lafiya mai tsanani, duk da haka ta kasa amfani da jikinta kuma an saka mata injin da zai taimaka mata ta yi numfashi. Ta yi ꞌyan kwanaki ta kasa tuna kome, ba ta ma tuna ko ita waye ba ce.

 Virginia ta bayyana abin da ya faru bayan haka. “Da sannu a hankali na soma tuna abubuwa. Na yi adduꞌa da dukan zuciyata. Ba na so in mutu in bar dana karami babu mahaifiya. Na yi kokari in tuna da ayoyin Littafi Mai Tsarki da yawa don in kasance da karfin zuciya.

 “A kwana a tashi na fita daga dakin jinya na musamman. Bayan na yi wata shida ina zuwa asibitoci dabam-dabam, sai na koma gida. Na kasa amfani da jikina gabaki daya, kuma na bukaci a taimaka min a kome da kome. Na yi bakin ciki! Na ji kamar ba ni da amfani ga mutane da kuma Jehobah. Na damu ko waye ne zai kula da dana.

 “Na soma karanta labaran wasu shaidun Jehobah da suke rashin lafiya mai tsanani kamar ni, kuma na yi mamaki don abubuwan da suka iya yi a hidimarsu ga Jehobah. Don haka na yi kokari in kasance da raꞌayin da ya dace ta wajen mai da hankali ga abin da zan iya yi. Kafin in soma ciwo, ba na samun lokaci don yin nazarin Littafi Mai Tsarki, da yin waꞌazi da kuma yin adduꞌa sosai. Yanzu a kowane lokaci zan iya yin hakan. Don haka, a maimakon in yi sanyin gwiwa, na mai da hankali a kan hidimata ga Jehobah.

 “Na koyi yadda zan yi amfani da kwamfuta. Nakan yi rubutu da manhajar da ke gane motsin kaina. Motsa kaina yakan gajiyar da ni, amma fasahar tana taimaka min in iya nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma waꞌazi ta wajen rubuta wasiku da sakonnin imel. Ina da allo kusa da ni mai harufa a kai, kuma da shi nake iya magana da mutane. Wanda yake tare da ni zai taba harufan daya bayan daya. Nakan wāre ido idan aka taba harufan da ba daidai ba, sai in kulle idanuna idan aka taba wanda ina so. Muna maimaita hakan don mu iya fito da kalmomi da jimloli. Wasu ꞌyanꞌuwa mata da suke yawan kasance tare da ni sukan san abin da ina son in fada kafin in fade su. A wasu lokuta, idan sun kasa gane abin da nake son in fada sai mu mai da shi abin dariya.

Tana magana ta wurin yin amfani da allo da ke dauke da harufa

 “Ina jin dadin yin ayyukan ibada tare da ikilisiya. Ba na fasa halartan taro ta naꞌura. Nakan rubuta kalamaina sai wani ya karanta su idan ana gudanar da sashe da ke da tambayoyi. Nakan kalle Tashar JW da wani karamin rukunin ꞌyanꞌuwa. a

 “Na yi shekaru 23 yanzu ina fama da wannan ciwon. A wasu lokuta nakan yi bakin ciki. Amma abubuwa da ke taimaka min in daina bakin ciki su ne yin adduꞌa, da yin cudanya da ꞌyanꞌuwa da kuma yin himma a hidimar Jehobah. Da taimakon ꞌyanꞌuwa na iya na yi hidimar majagaba na dan lokaci na fiye da shekaru shida yanzu. Na yi kokari in kafa wa dana mai suna Alessandro misali mai kyau, wanda ya yi aure yanzu kuma dattijo ne. Kari ga haka, yana hidimar majagaba tare da matarsa.

 “Ina yawan yin bimbini a kan abubuwan da zan iya yi a aljanna da ke zuwa. Abu na farko da ina son in yi shi ne in yi magana game da Jehobah da muryata. Zan so in yi tafiya a wurin da ruwa ke kwararowa don in gan kyaun filin da ke kewaye da wurin. Kuma da yake yanzu na yi shekaru ashirin ana ba ni abinci ta tiyo, ina marmarin lokacin da zan iya tsinke aful da kaina in ci. Kari ga haka, ni ꞌyar Italiya ce kuma ina marmarin lokacin da zan iya dafa abincin Italiya da na fi so, kamar pizza!

 “‘Sa zuciya ga samun ceto’ ya taimaka min in kare tunanina. (1 Tasalonikawa 5:8) Yin tunani cewa ina sabuwar duniya yana sa ni farin ciki duk da cewa ina rashin lafiya, kuma na san cewa nan ba da dadewa ba zan warke. Hakika ina dokin more ‘ainihin rai’ da Jehobah ya yi alkawari cewa zai ba mu ta wurin Mulkinsa.”​—1 Timoti 6:19; Matiyu 6:​9, 10.

a Za ka iya shiga Tashar JW ta dandalin jw.org.